Sababbin bayanai sun nuna larurar mantuwa ta sa dole Alkalin Alkalan Kasa yin murabus

Sababbin bayanai sun nuna larurar mantuwa ta sa dole Alkalin Alkalan Kasa yin murabus

  • Ana tunanin matsalar rashin lafiya ne ya jawo Tanko Muhammad ya sauka daga kujerar da yake kai
  • Alkalin Alkalan ya rubuta takardar murabus, wannan mataki da ya dauka ya ba mutane mamaki
  • CJN Tanko Muhammad ya yi ta fama da larura, har abin ya fara bayyana a wajen gudanar da aikinsa

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Wasu sababbin bayanai su na kara fitowa a game da dalilin da ya sa Tanko Muhammad ya rubuta takardar murabus, ya sauka daga kan kujerar CJN.

The Nation a rahoton da ta fitar a ranar Talata, 28 ga watan Yuni 2022, ta tabbatar da cewa ba murabus din Allah da AnnabinSa, Tanko Muhammad ya yi ba.

Ya kamata sai karshen Disamban 2024 ne Tanko Muhammad zai ajiye aiki, amma a karshe sai aka ji labari ya aika takardar murabus, ya hakura da mukaminsa.

Kara karanta wannan

Gaskiya Tayi Halinta: Yadda Aka Tirsasa CJN Tanko Yayi Murabus Kan Dole

Ana zargin cewa larurar da ke damun Muhammad ne ta jawo ya rubuta takardar murabus alhali yana da ragowar shekara daya da rabi da ya rage masa a bakin aiki.

Ana samun matsala a ofis

Muhammad da aka nada tun 2019 yana fama da matsalar cutar mantuwa, wannan ya sa ya gaza gudanar da aikin ofishinsa na Alkalin Alkalan kasa da kyau.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Rahoton ya ce babban Alkalin na Najeriya ya rika fuskantar matsaloli wajen gudanar da bincike na harkar shari’a a matsayinsa na shugaban kotun koli na kasa.

Alkalin Alkalai
Tsohon Alkalin Alkalai na Kasa Hoto: www.channelstv.com
Asali: UGC

Amma duk da haka ya cigaba da zama a kujerarsa saboda gudun wasu su rika juya babban kotun Najeriya, wanda hakan zai iya jefa kasar a tirka-tirkar shari’a.

Bugu da kari, likitoci sun fadawa Alkali Muhammad da cewa ya rika bi sannu a hankali da jikinsa.

Kara karanta wannan

Muhimman abubuwa 10 da ya kamata ku sani game da tsohon shugaban alkalan Najeriya Tanko Muhammad

Tsoron Mary Odili ta zama CJN

Ana zargin tun a shekarar da ta wuce, Muhammad ya nemi ya ajiye wannan aiki, amma aka hana shi yin hakan saboda Mary Odili ta zama CJN kafin tayi ritaya.

Wata majiya ta ce tun da ya karbi aiki daga hannun tsohon Alkalin Alkalai, Walter Onnoghen, Mai shari’a Tanko Mohammed yake fama da matsalar rashin lafiya.

Har abin ya kai Alkalin Alkalan bai iya halartar wasu taro, aka dauki tsawon lokaci a wannan hali. Abin bai cabe ba sai da Alkalan kotun koli suka fara yin korafi.

Shawarar Ango Abdullahi

An samu labari Ango Abdullahi ya ce shekara 25 ko 30 kenan, babu abin da Atiku Abubakar da Bola Tinubu suka yi wa al’umma, ya ce ba za su iya gyara kasa ba.

Amma kuma Farfesa Ango ya ce Sanata Rabiu Kwankwaso mutumin kirki ne wanda ya dade a harkar siyasa, kuma bai samu wata makusa a game da Peter Obi ba.

Kara karanta wannan

Rashawa? Dalilai masu karfi guda 5 da suka sa shugaban alkalai ya ajiye aikinsa

Asali: Legit.ng

Online view pixel