Na yi mafarki zan yi kudi idan na shafe kaina da jininsa, in ji mutumin da ya sare kan dansa

Na yi mafarki zan yi kudi idan na shafe kaina da jininsa, in ji mutumin da ya sare kan dansa

  • Wani magidanci mai suna Mista Volt Blessing Gabriel, dan shekaru 33 ya shiga hannun yan sanda a jihar Delta bisa zargin kashe dan cikinsa
  • Gabriel dai ya ce ya yi mafarki da wani mutum ne idan ya fada masa cewa zai yi kudi idan har ya shafa jinin dan nasa a kansa
  • Tun farko dai mahaifiyar yaron ce ta kai karar mijin nata ofishin yan sanda bayan ta gaza ganin dan nata sannan mai gidan nata ya yi mata yawo da hankali

Delta - Jami’an yan sandan jihar Delta sun kama wani mutum mai shekaru 33, Mista Volt Blessing Gabriel, kan amfani da zarto wajen sare kan dansa mai shekara daya don yin asirin kudi.

Gabriel wanda ya kashe dan nasa mai suna Godspower a jeji a garin Benin, jihar Edo, ya binne kan mamacin a kusa da wata bishiyar kwakwa sannan ya jefar da gawar, jaridar Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

Ba zan bar harkar siyasa ba, mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ga magoya bayansa

An tattaro cewa mai laifin ya ce ya kashe yaron ne saboda ya yi mafarki cewa idan ya aikata hakan, sannan ya shafe kansa da jinin, zai yi arziki.

Jami'an yan sanda
Na yi mafarki zan yi kudi idan na shafe kaina da jininsa, in ji mutumin da ya sare kan dansa Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Kakakin yan sandan jihar Delta, Mista Bright Edafe, wanda ya tabbatar da lamarin a cikin wata sanarwa, ya ce an kama Gabriel ne bayan matarsa ta gano batan dan nata sannan ta kai rahoton cewa tana zargin mijin nata.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kamar yadda jaridar Independent ta rahoto sanarwar ta ce:

“A ranar 25/06/2022, da misalin karfe 10:30, wata Misis Success Oduwa mai shekaru 24 a mararrabar Peanuts, Obeh a jihar Edo, ta gano cewa bata ga danta ba tun da safiyar 24/06/2022 sannan sai ta fara damun mijinta kan ina danta yake.
“Mijin nata ya sanar da ita cewa dan na tare da yar’uwarsa a Warri. Da isarta Warri, sai ta gano cewa mijin nata karya ya yi mata, don haka sai ta fara zarginsa.

Kara karanta wannan

Manyan Sirruka Sun Sake Bayyana Kan Yaron Da Ekweremadu Ya Kai UK Don Cire Masa Koda

“Sai ta kai rahoton lamarin ga kwamandan RRS, cewa tana zargin mijinta mai suna Volt Blessing Gabriel mai shekaru 33, wanda ke a adireshi daya da ita ya kashe masu dansu mai suna Godspower Gabriel, mai shekara daya da wata takwas a duniya don kudin asiri.
“Sai kwamandan RRS ya ba jami’ansa bayani, inda suka shiga aiki, suka kama mijin sannan suka mika shi ga DPO na sashin ‘A’ Division Warri don ci gaba da bincike.
“Da ake masa tambayoyi, sai wanda ake zargin ya ce shi ya kashe dan a jejin Ewabogun hanyar katolika, birnin Benin, ta hanyar amfani da zarto wajen fille masa kai sannan ya binne shi a kusa da wata bishiyar kwakwa da ke dajin ya kuma jefar da gawar yaron mara kai.
“Wanda ake zargin ya kuma bayyana cewa ya kashe yaron ne saboda yayi mafarki, inda ya ga wani mutum wanda ya fada masa cewa idan ya kashe yaron sannan ya goga jininsa a kansa, zai zama mai kudi. Wanda ake zargin yana tsare.”

Kara karanta wannan

Katsina: Rundunar Yan Sanda Ta Karrama Jami'inta Da Dawo Da Makuden Daloli Da Ya Tsinta a Sansanin Alhazai

Yan bindiga sun kashe wani malamin addini a jihar Kaduna

A wani labari na daban, mun ji cewa wasu yan bindiga sun kashe babban malamin darikar Katolika na kwalejin fasaha ta jihar Kaduna, Rev. Fr. Vitus Borogo a ranar Asabar, 25 ga watan Yuni, a gonarsa da ke hanyar Kaduna-Kachia.

Shugaban darikar Katolika a jihar Kaduna, Rev. Fr. Christian Emmanuel, ya tabbatar da faruwa lamarin a wata sanarwa da aka gabatarwa kamfanin dillancin labaran Najeriya a Kaduna.

Emmanuel ya ce an kashe Marigayi Borogo a gonar gidan yari, Kujama, hanyar Kaduna zuwa Kachia, bayan wasu da ake zaton yan ta’adda ne sun farmaki gonar, jaridar The Guardian ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel