Manyan Labarai A Yau
Wata matar aure ta ɗauki matakin ladabtarwa kan ɗanta bayan ya kawo budurwarsa gida. Matar auren ta fusata inda ta yi masa wanka da tafasashshen ruwan zafi.
Miyagun ƴan bindiga sun farmaki garin Jere na jihar Kaduna inda suka halaka bayin Allah, da sace mutane masu yawa. Ƴan bindigan sun zo ne da manyan makamai.
Wani ginin bene ya rufto kan ma'aikatansa a jihar Anambra inda ya salwantar da rayukan mutum uku. Ma'aikatan na shirin fara aiki ne lokacin da ginin ya rufto.
Batun cewa shugaban mulkin sojin Mali ya yi barazanar farmakar birnin Abuja tare da ɗora ainihin wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasa kan mulki ba gaskiya ba ne.
Rundunar yan sandan jihar Kano ta sanar da fara gudanar da bincike a kan rade-radi da ke yawo na zargin bullar wasu mata masu shiga gidan mutane suna shan jini.
Wani mummunan hatsarin mota ya ritsa da wasu bayin Allah a jihar Osun. An salwantar da rayukan mutane masu yawa a dalilin hatsarin motar da ya auku cikin dare.
Gwamnatin Neja ta bayyana cewa tana shirin farfado da tsarin bai wa daliban jihar da ke karatu a jami’a kudin tallafi domin rage radadin halin da ake ciki.
An shiga jimamin rasuwar tsohon kwamishinan gidaje na jihar Legas, Bosun Jeje wanda ga riga mu gidan gaskiya a ranar Asabar, 2 ga watan Agustan 2023 a Legas.
Tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ya musanta cewa ya amince da bayar da kwangilar $6bn ta samar da wutar Mambilla ga kamfanin Sunrise Power a shekarar 2003
Manyan Labarai A Yau
Samu kari