Budurwa Ta Rabu Da Matashin Da Ya Bude Mata Shago Bayan Ya Samu Karayar Arziki

Budurwa Ta Rabu Da Matashin Da Ya Bude Mata Shago Bayan Ya Samu Karayar Arziki

  • Wata budurwa ta rabu da matashin da ya taimaka mata bayan ta fahimci ya samu karayar tattalin arziƙi
  • Budurwar sai ta fara soyayya da ɗaya daga cikin kwastomominta, inda ta rabu da wanda ya taimaka mata
  • Matashin yanzu ya farfaɗo arziƙinsa ya dawo, kuma budurwar ta dawo wajensa, amma yana ɓata mata lokaci ne kawai

Wani matashi wanda bai ji da daɗi ba a hannun wata budurwa wacce ya taimaka a baya, ya dawo domin ɗaukar fansa.

Matashin shi ne ya taimaka mata ta buɗe shagon siyar da kayan sawa, amma daga baya sai budurwar ta rabu da shi.

Budurwa ta rabu da wanda ya taimaka mata
Budurwar ta dawo bayan arzikinsa ya dawo Hoto: Getty Images/Hill Street Studios and Vladimir Vladimirov (Hotunan an yi amfani da su ne kawai domin misali)
Asali: Getty Images

Bayan shagon na ta ya fara bunƙasa, sai arziƙin matashin ya yi ƙasa ya samu tawayar arziƙi, sai kawai budurwar ta rabu da shi ta koma wajen wani saurayin na daban.

Kara karanta wannan

"Gobe Ka Kara": Matar Aure Ta Kwarawa Dan Cikinta Tafasashshen Ruwan Zafi Bayan Ya Aikata Wani Abu 1

Sabon saurayin na ta dai wani kwastomanta ne wanda ya zo shagonta domin yin siyayya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matashi ya ɗauki fansa kan budurwar da ta rabu da shi

A wani labari mai sosa zuciya da Wizarab ya sanya a shafinsa na X (wanda a baya aka sani da Twitter, matashin ya bayyana cewa yanzu arziƙinsa ya dawo.

Ya koma yanzu suna soyayya da budurwar da ta rabu da shi, inda kawai yake ɗaukar fansa a kanta ta hanyar ɓata mata lokaci da ƙin yarda ya riƙa kashe mata kuɗi.

A kalamansa:

"Yanzu arziƙinsa ya dawo fiye da na baya. Sannan budurwar ta dawo wajensa tana cin amanar kwastomanta tare da shi. So yake yi ya gama da ita gaba ɗaya. Bai kashe mata ko sisi."

Ƴan soshiyal midiya sun yi martani

@Kenkelinke ta rubuta:

Kara karanta wannan

Abin Mamaki: Wata Akuya Ta Haifi Rabi Mutum Rabi Akuya a Wata Jihar Arewa, Bidiyonta Ya Yadu

"Idan har tsanar da na yi ta kai na aikata hakan, gwara na rabu da ita gaba ɗaga, saboda wannan wauta ce babba."

@Antone401 ya rubuta:

"Ta iya yiwuwa ma ba son shi take yi ba. Kawai tana son zama ne kusa da kuɗi."

@Ezigbopikin ya rubuta:

"Irin ɗaukar fansa ta kenan."

@Mr_Nobodie0 ya rubuta:

"Ɗaukar fansa akwai daɗi."

Kyakkyawar Budurwa Na Neman Mijin Aure

A wani labarin kuma, wata kyakkayawar budurwa tana mijin da za ta aura su raya Sunnah ido rufe.

Budurwar ta kafa sharaɗin cewa wanda duk zai so ta da aure sai ya shirya, inda ta bayyana cewa dole sai yana samun albashin N300k duk wata, sannan ya mallaki motar kansa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel