Manyan Labarai A Yau
Wani matashi ya nuna hirar da suka yi da tsohuwar budurwarsa wacce suka rabu. Budurwar ta yi magana bayan ta ga ya siyo sabuwar mota inda ta nemi su sasanta.
Wani mummunan hatsarin mota da ya auku a jihar Ondo, ya salwantar da rayukan mutum. Wasu mutum biyar kuma sum samu munanan raunika a dalilin hatsarin motar.
Tsagerun yan bindiga sun farmaki wasu masallata a wani masallaci a kauyen Saya-Saya da ke karamar hukumar Ikara ta jihar Kaduna, inda suka kashe mutum bakwai.
Gwamnatin Dauda Lawal na jihar Zamfara ta yi watsi da ikirarin ta bayar da umurnin sakin matan wasu yan bindiga biyu. Ta ce babu yadda za a yi ta yarda da haka.
Dan Najeriya yana cikin farin ciki bayan ya samu kudi naira miliyan 36 saboda ya yi amfani da Twitter na wata daya, hakan na zuwa bayan Elon Musk ya kawo sauyi.
Hankula sun tashi bayan wani basarake ya tilasta matasa sun saki matan ƴam bindigan da suka kama a jihar Zamfara bayan sun sace musu mutum shida A ƙauyensu.
Gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu Sokoto ya amince da sakin kudi kimanin naira biliyan 4 don siyan kayan abinci da za a raba a fadin kananan hukumomin jihar.
Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya bayyana cewa ya ji dadin abun da ya faru a Gabon bayan sojoji sun kwace mulki a kasar mai arzikin man fetur.
Wani dan Najeriya a kasar Birtaniya ya makale bayan matarsa da ke cin amanarsa ta soke bizarsa. An ba shi wa’adi ya gyaro lamarin ko a kore shi gida Najeriya.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari