Gwamnatin Jihar Katsina Ta Kaddamar Da Sabon Shirin Rabon Kayan Tallafi

Gwamnatin Jihar Katsina Ta Kaddamar Da Sabon Shirin Rabon Kayan Tallafi

  • Gwamnatin jihar Katsina ta fara sabon rabon kayan tallafi domin rage raɗaɗin cire tallafin man fetur da aka yi a ƙasar nan
  • Gwamnatin ta ƙaddamar da rabon kayan tallafin ne a ƙaramar hukumar Kankara ya jihar a ƙarƙashin jagorancin mataimakin gwamnan jihar
  • Gwamnatin ta bayyana cewa a sabon rabon tallafin kowace rumfunar zaɓe cikin rumfunan zaɓen jihar za ta samu buhunan shinkafa biyar

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Katsina - Gwamnatin jihar Katsina a ranar Lahadi, 3 ga watan Satumba ta ƙaddamar da rabon tallafi a ƙaramar hukumar Kankara ta jihar.

Haka na zuwa ne bayan gwamnatin tarayya ta tsige tallafin man fetur, wanda hakan ya sanya tsadar rayuwa da tashin kuɗin kayan abinci da sauran kayan masarufi ya ƙaru a ƙasar nan.

Gwamnatin Katsina ta fara rabon kayan tallafi
Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda Hoto: @dikko_radda
Asali: Twitter

Mataimakin gwamnan jihar Katsina, Hon. Faruk Lawal Jobe, shi ne ya ƙaddamar da rabon kayan tallafin a ƙaramar hukumar Kankara ta jihar.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Hukumar DSS Ta Bankado Shirin Tayar Da Tarzoma a Kasa, Ta Magantu Kan Masu Hannu a Ciki

Yadda za a yi rabon tallafin

Faruk ya yi bayanin cewa rabon tallafin za a gudanar da shi a gundumomi 361 na jihar inda kowane akwatun zaɓe daga cikin akwatuna 6,652 a jihar za a bayar da buhunan shinkafa biyar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mataimakin gwamnan ya buƙaci jama'a da su yi amfani da kayan tallafin yadda ya dace inda ya roƙe su da su tabbatar cewa masu ƙaramin ƙarfi da ke a cikinsu ne suka samu gajiyar kayan tallafin.

A kalamansa:

"Waɗannan kayan tallafin za a raba su ne a akwatunan zaɓe, ƙaramar hukumar Kankara tana da gundumomi 11 da rumfunan zaɓe 256."
"Wannan tallafin ya bambanta da wanda shugabannin ƙananan hukumomi suka fara rabawa bisa umarnin da gwamna Malam Dikko Radda, ya ba su na siyo masara domin rabawa kyauta ga al'umma."

Kara karanta wannan

Gwamna Uba Sani Ya Dau Zafi Kan Kisan Masallata a Kaduna, Ya Ba Jami'an Tsaro Muhimmin Umarni

Gwamna Dikko Ya Tuna Da Iyalan Yan Sakai

A wani labarin na daban kuma, gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda ya tuna da iyalan ƴan sakan da suka ransu a wajen kare jihar, inda ya raba musu maƙudan kuɗaɗe.

Gwamnan Dikko ya raba N20m ga iyalan ƴan sakai 33 da suka bayar da rayuwarsu wajen ganin zaman lafiya ya ɗore a jiharta Katsina.

Asali: Legit.ng

Online view pixel