Mutum 3 Sun Riga Mu Gidan Gaskiya Bayan Wani Gini Ya Rufto a Anambra

Mutum 3 Sun Riga Mu Gidan Gaskiya Bayan Wani Gini Ya Rufto a Anambra

  • Wasu bayin Allah masu neman halaliyarsu sun riga mu gidan gaskiya bayan wani ginin bene ya rufto musu a jihar Anambra
  • Mutum uku ne suka rasu waɗanda suka haɗa da wani mahaifi da ƴaƴansa guda biyu masu aiki a wajen
  • Shugaban hukumar COREN ta jihar ya ɗora alhakin ruftowar ginin benen a kan amfani da kayan aiki marasa inganci

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Anambra - Wani bene da ake aikin gininsa ya rufto a Egbu Umuenem, a gundumar Otolo Nnewi, a ƙaramar hukumar Nnewi ta Arewa a jihar Anambra.

Jaridar The Punch ta rahoto cewa ginin ya rufto ne da misalin ƙarfe 1:00 na daren ranar Lahadi lokacin da ma'aikatan da ke aiki a wajen ke barci domin fara aikinsu idan gari ya waye.

Ginin bene ya rufto a Anambra
Ginin benen da ya rufto kan ma'aikata Hoto: Punchng.com
Asali: UGC

Mutum uku waɗanda suka haɗa wanu mahaifi da ƴaƴansa biyu, waɗanda za a yi aikin tare da su sun mutu nan take a wajen, yayin da sauran ma'aikatan suka samu raunika.

Kara karanta wannan

Abin Mamaki: Wata Akuya Ta Haifi Rabi Mutum Rabi Akuya a Wata Jihar Arewa, Bidiyonta Ya Yadu

Shaidun gani da ido sun bayyana cewa sauran mutanen da suka maƙale a ɓuraguzan ginin, an samu ceto su inda aka garzaya da su zuwa asibitin St. Felix da ke a Nnewi, rahoton The Nation ya tabbatar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Ginin ya rufto ne da misalin ƙarfe 1:00 na daren ranar Lahadi, inda ya yi wata ƙara mai tsawatarwa. Mutum uku, mahaifi da ƴaƴansa biyu waɗanda ke cikin ma'aikatan da za su yi aiki a wajen sun rasu. Sun zo ne daga ƙauyen Nimo." A cewar shaidar.

Dalilin da ya haddasa ruftowar ginin

Da yake jawabi ga manema labarai jim kaɗan bayan an ciro gawarwakin mutanen da suka rasu, shugaban hukumar COREN ta jihar, Victo Meju ya ɗora alhakin ruftowar ginin kan yin amfani da kayan aikin waɗanda ba su da inganci da rashin samun izni daga hukumomi.

Kara karanta wannan

Subhanallahi: Rayuka Da Dama Sun Salwanta a Wani Mummunan Hatsari Da Ya Auku a Wata Jiha

Ya sanar da kulle wajen, inda ya ƙara da cewa za a gayyato mamallakin ginin, Chukwunafu Anamanjo domin amsa tambayoyi waɗanda za su taimaka wajen gudanar da bincike.

Bene Ya Rufto a Abuja

A wani labarin kuma, wani makeken bene mai hawa biyu ya rufto a birnin tarayya Abuja, cikin tsakar dare.

Benen wanda ya rufto a gundumar Garki II ta birnin tarayya Abuja ya rufto a dalilin ruwan sama kamar da bakin ƙwarya inda ya ritsa da mutane masu yawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel