“Tesla Da Benz”: Dan Najeriya Da Ke Zaune a Turai Ya Yi Bidiyon Tsadaddun Motocin Da Ake Tasi Da Su

“Tesla Da Benz”: Dan Najeriya Da Ke Zaune a Turai Ya Yi Bidiyon Tsadaddun Motocin Da Ake Tasi Da Su

  • Wani dan Najeriya ya bukaci mamallakan motocin Benz da Tesla da su zamo masu kankan da kai domin da irin su ake tasi a turai
  • A cikin wani bidiyo da ya wallafa a TikTok, mutumin mai suna Emeka Prosper, ya ce ya ga tsadaddun motocin alfarma da logon tasi suna jiran fasinjoji
  • Bidiyon ya nuno motocin Mercedes Benz da Tesla dauke da alamun tasi, amma mutumin bai bayyana ko a wace kasa ya dauki bidiyon ba

Wani dan Najeriya da ke zaune a turai ya cika da mamaki lokacin da ya ga wasu tsadaddun motocin alfarma baje a titi a matsayin tasi.

A wani bidiyo da ya yada, mutumin mai suna Emeka Prosper, ya nunawa mabiyansa manyan motoci kamar su Mercedes Benz da Tesla da aka paka a kan hanya.

Kara karanta wannan

‘Yan Bindiga Sun Bude Wuta a Titi, Sun Yi Awon Gaba da Mutane a Hanyar Abuja

Dan Najeriya ya yi mamakin yadda ake tasi da manyan motocin alfarma a Turai
“Tesla Da Benz”: Dan Najeriya Da Ke Zaune a Turai Ya Yi Bidiyon Tsadaddun Motocin Da Ake Tasi Da Su Hoto: TikTok/@mekusunique12.
Asali: TikTok

Mutumin ya ce wadanda suka mallaki irin wadannan motoci a gida su zamo masu kankan da kai saboda da irin motocin ne mutane suke hawa a matsayin tasi a turai.

Ana amfani da motocin Tesla da Mercedes Benz a matsayin tasi

A cikin bidiyon, motocin na dauke da logon tasi, kuma an paka su a bakin hanya inda suke jiran fasinjoji.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai kuma wasu da suka ga bidiyon sun bayyana cewa don ana amfani da tsadaddun motoci a matsayin tasi a wasu wuraren, baya nufin kada wadanda suka mallake su a gida su yi farin ciki.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani yayin da ake amfani da Tesla da Mercedes Benz a matsayin tasi

@Iamphilix ya ce:

"Tasi ko ba tasi ba, sai ka zamo mai kudi sosai kafin ka iya siyan irin wadannan motocin a chan. Ba na talaka bane."

Kara karanta wannan

Baturiya Ta Saki Hotuna Yayin da Ta Fallasa Masoyinta Dan Najeriya Wanda Ya Barta Da Ciki a Turai Don Auren Yar Najeriya

@thehumblemaster ya tambaya:

"Sun fada maka cewa saboda suna amfani da ita a matsayin tasi kowa da ke nan ne zai iya mallakar ta?"

@chidigodwin903 ya ce:

"Yallabai da alama karo na farko kenan da take tafiya. A Dubai suna amfani da sabbin motocin 2023 a matsayin tasi."

@Terry Martin ya yi martani:

"A halin da ake ciki a nan Afrika, matasa da dama sun kashe iyayensu mata da maza don kawai su siya tasi."

@Wizzy Cwc ya tambaya:

"Amma dan uwa, wacce kasa ce wannan? Ina so na zo chan don Allah."

Matashi ya siya mota da albashinsa na farko a Canada

A wani labarin kuma, mun ji cewa wani dan Najeriya da ke zaune a kasar Canada ya siyawa kansa sabuwar mota kirar Honda Civic, kuma ya garzaya dandalin TikTok don yin murna.

Mai motar, Abwire, ya wallafa bidiyon motar a dandalinsa na TikTok, kuma abokai da mabiyansa sun taya shi murna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel