Hukumar DSS Ta Bankado Shirin Gudanar Da Zanga-Zangar Tayar Da Tarzoma

Hukumar DSS Ta Bankado Shirin Gudanar Da Zanga-Zangar Tayar Da Tarzoma

  • Hukumar ƴan sandan farin kaya (DSS) a ranar Litinin, 4 ga watan Satumba, ta bayyana cewa ta bankaɗo shirin wasu ƴan siyasa na shirya zangar-zangar tayar da tarzoma
  • DSS ta bayyana cewa an shirya zanga-zangar ne domin a ɓata sunan gwamnatin Tinubu kan abubuwan da suka shafi tattalin arziƙi
  • DSS ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da kakakin hukumar, Peter Afunanya ya rattaɓawa hannu

FCT, Abuja - Hukumar ƴan sandan farin kaya (DSS) a ranar Litinin, 4 ga watan Satumba ta bayyana cewa ta bankaɗo wani shirin yin zanga-zangar tayar da tarzoma domin ɓata sunan gwamnatin tarayya da jami'an tsaro kan abubuwan da suka shafi tattalin arziƙi.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin hukumar, Peter Afunanya, ya rattaɓawa hannu.

Kara karanta wannan

Atiku, Tinubu Da Obi Za Su San Makomarsu Yayin Da Kotun Zaɓe Ta Sanar Da Lokacin Yanke Hukunci

DSS ta bankado shirin tayar da tarzoma
Hukumar DSS ta bankado shirin tayar da tarzoma a kasa Hoto: @OfficialDSSNG
Asali: Twitter

DSS ta bankaɗo shirin yin zanga-zanga

Hukumar ta bayyana cewa ta gano masu kitsa wannan mummunan ƙullin, sannan tana nan tana sanya musu ido.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

DSS ta ce bayanan sirri sun nuna cewa daga cikin jagororin da ke kan gaba wajen shirin akwai wasu ƴan siyasa waɗanda su ke tattaro shugabannin ɗalibai, matasa, ƙungiyoyin ƙabilu, da masu jin zafin gwamnati domin gudanar da zanga-zangar.

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

"Hukumar ta gano shugabannin da ke kitsa wannan shirin, tare da ƙara sanya ido a kansu domin hana su jefa ƙasar nan cikin hargitsi."

Haka kuma hukumar ta shawarci shugabannin jami'o'i da sauran makarantun gaba da sakandire da hana ɗalibansu, shiga cikin duk wasu abubuwa da ka iya kawo rashin zaman lafiya a ƙasa.

Hukumar DSS ta cigaba da cewa:

Kara karanta wannan

Abin Mamaki: Wata Akuya Ta Haifi Rabi Mutum Rabi Akuya a Wata Jihar Arewa, Bidiyonta Ya Yadu

"Haka kuma, hukumar na shawartar iyaye da su yi kira ga ƴaƴansu kan su guji shiga duk cikin abubuwan da suka saɓa wa doka da oda."
"A yayin da DSS take sane da ƙoƙarin gwamnati da jajircewarta wajen magance wasu daga cikin matsalolin da suka addabi ƙasa, tana gargaɗi ga masi son kawo hargitsi da su shiga taitayinsu. Hakan ya zama wajibi domin ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen tuhumar masu shirya wannan mummunan shirin."

DSS Ya Cafke Manajojin Jirgin Kasan Kaduna-Abuja

A wani labarin kuma, hukumar DSS ta yi caraf da Manajan da ke kula da harkokin sufurin jirgin ƙasan Kaduna-Abuja.

Hukumar ta cafke Pascal Nnorli biyo bayan fitar kundin gargaɗi kan yiwuwar kai farmakin ƴan bindiga. An cafke Pascal tare da wani Manajan da kuma wasu ma'aikata saboda fitar bayanan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel