Manyan Labarai A Yau
Rundunar ƴan sandan jihar Legas ta tabbatar da cafke mawaƙi Azeez Fashola wanda aka fi sani da Naira Marley domin amsa tambayoyi kan mutuwar tsohon yaronsa Mohbad.
Majalisar dattawan Najeriya ta yi wa dokokinta sabon garambawul inda ta haramtawa sabbin sanatoci tsayawa takarar shugaban majalisa da mataimakinsa.
Shugaban cocin Fire of Liberation Interdenominational Ministries, fasto Fabian Nna, bai tayar da matacce ba daga cikin akwati kamar yadda ake cewa.
An shiga jimami da takaici bayan wani jirgin ruwa ɗauke da fasinjoji ƴan kasuwa ya kife a cikin kogi a jihar Kebbi. Mutane da dama sun nutse a hatsarin.
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya aike da wasiƙa zuwa ga majalisar dattawan Najeriya domin neman amincewarta kan ministoci uku da ya ƙara naɗa wa.
Ɗaliban jami'ar Obafemi Awolowo da ke Ile-Ife a jihar Osun, sun kulle ƙofar shiga harabar jami'ar domin nuna adawarsu kan ƙarin kuɗin makarantar da aka yi.
Ana shari’a tsakanin Diezani Alison-Madueke da gwamnatin Birtaniya a wani kotu da ke Westminster. Tun da tsohuwar ministar ta bar gwamnati ake wasan kura da ita.
Kungiya ta zargi Abba Yusuf da jam’iyyar New Nigerian Peoples Party (NNPP) da daukar nauyin mutane a kasar waje domin yin zanga-zanga kan bangaren shari’ar Najeriya.
An bayyana labarin wani shahararren farfesan Najeriya daga jamni’ar Najeriya wanda ya fara da gwagwarmayar rayuwa amma ya ki saduda har sai da ya cimma nasara.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari