Jerin Gwamnonin Da Kotu Ka Iya Kora a Cikin Watan Oktoba

Jerin Gwamnonin Da Kotu Ka Iya Kora a Cikin Watan Oktoba

Kotunan sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnoni a jihohi 28 da aka gudanar da zaben gwamnoni a ranar 18 ga watan Maris, sun fara saurare da yanke hukunci a faɗin jihohin.

Kamar yadda dokar zaɓe ta 2022 ta tanada, an wajabta wa kotunan zaɓen su saurari ƙara tare da yanke hukunci a cikin kwanaki 180.

Gwamnonin da aka iya rasa kujerunsu a watan Oktoba
Gwamnonin da kotu ba ta yi hukunci kan nasararsu ba Hoto: Alex Otti/Babagana Zulum/Nasir Idris
Asali: Twitter

Ya zuwa yanzu dai gwamnoni 20 daga cikin 28 sun san makomarsu a kotu. An tabbatar da zaben gwamnoni 18, yayin da kotun sauraron ƙararrakin zaɓe ta kori gwamna Abba Kabir Yusuf na Kano da Abdullahi Sule na Nasarawa.

Sai dai, ana sa ran kotunan za su tantance makomar gwamnoni takwas ta hanyar korarsu ko kuma tabbatar da nasararsu a zaɓen 2023.

Ga jerin sunayen gwamnonin:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Abubuwan da Ya Kamata Ku Sani Game da Ɗan Takarar PDP Da Kotu Ayyana a Matsayin Gwamnan Nasarawa

Alex Otti na Abia

Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan jihar Abia ta sanya ranar Juma'a, 6 ga watan Oktoba domin yanke hukunci kan makomar gwamnan jam'iyyar Labour Party.

Otti dai yana fuskantar ƙalubale daga daga ɗan takarar jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Cif Ikechi Emenike, kan rashin yin murabus kafin ya koma jam'iyyar Labour Party.

Babagana Zulum na Borno

Ana ƙalubalantar nasarar gwamna Babagana Zulum na jihar Borno a gaban kotun sauraron ƙararrakin zaben gwamnan jihar, kuma kotu na iya yanke hukuncin a cikin wannan watan.

Umar Alkali da jam'iyyarsa ta New Nigeria Peoples Party (NNPP) suna neman kotu da ta ba da umarnin sake gudanar da zabe a jihar saboda cire sunayensu a cikin takardar ƙuri'a a lokacin zaɓe.

Mal Umar Namadi Namadi na Jigawa

Gwamnan jihar Jigawa Umar Namadi na jam'iyyar APC ya lashe zaben gwamnan jihar da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Kotu Ta Karanto Hukunci Kan Nasarar Gwamnan PDP, Ta Tabbatar da Wanda Ya Ci Zaɓe

Jam’iyyar PDP ta yi watsi da nasarar Namadi a jihar, sai dai ba a iya tantance ko ƴan adawa sun ƙalubalanci sakamakon a kotun.

Dr Dikko Umar Radda na Katsina

An ayyana gwamna Dikko Umar na Katsina a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamna na shekarar 2023 a jihar.

Jam'iyyar adawa ba ta ƙalubalanci ko fatali da nasarar da ya samu ba a zaɓen gwamnan jihar ta yankin Arewa maso Yamma.

Nasiru Idris na Kebbi

Nasarar Gwamna Nasir Idris da mataimakinsa Abubakar Umar Tafida da APC na fuskantar ƙalubale daga PDP da ɗan takararta, Aminu Bande.

Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan jihar da ke zamanta a Birnin Kebbi a kwanakin baya ta yi nuni da cewa nan ba da jimawa ba za ta yanke hukunci kan ƙarar da aka shigar a gabanta.

Sauran jihohin su ne:

1. Yobe

Kara karanta wannan

An Tsaurara Matakan Tsaro Yayin Da Gwamnan APC Ke Shirin Tantance Makomarsa a Kotun Zaɓe

2. Kwara

3. Neja

Kotu Ta Tabbatar Da Nasarar Gwamnan Sokoto

A wani labarin kuma, kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan jihar Sokoto, ta tabbatar da nasarar gwamna Ahmed Aliyu na jam'iyyar APC.

Kotun zaɓen ta yi fatali da ƙarar da ɗan takarar jam'iyyar PDP ya shigar yana ƙaluɓalantar nasarar gwamnan a kotu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng