Daliban OAU Sun Rufe Harabar Jami'ar, Sun Bukaci a Rage Kudin Makaranta

Daliban OAU Sun Rufe Harabar Jami'ar, Sun Bukaci a Rage Kudin Makaranta

  • Ɗaliban jami'ar OAU sun yi kira ga mahukuntan jami'ar da su rage kuɗin makaranta da kaso 50%
  • Ɗaliban a safiyar ranar Talata sun yi dafifi a babbar kofar makarantar domin neman a rage musu kuɗaɗen makaranta cikin gaggawa
  • Fusatattun ɗaliban sun rufe ƙofar harabar makarantar domin jawo hankalin mahukuntan jami'ar

Ile-Ife, jihar Osun - Ɗaliban jami’ar Obafemi Awolowo (OAU) da ke Ile Ife, Jihar Osun, sun rufe kofar shiga harabar jami'ar inda suka bukaci a rage kaso hamsin (50%) na kuɗin makaranta.

TVC News ta tabbatar da hakan a ranar Talata, 3 ga watan Oktoba, a shafinta na X (wanda a baya aka fi sani da Twitter).

Daliban OAU sun kulle jami'ar
Daliban OAU sun rufe jami'ar kan karin kudin makaranta Hoto: Aka Daniel
Asali: Facebook

Wacce buƙata ɗaliban ke nema?

Ɗaliban da sanyin safiyar Talata, 3 ga watan Oktoba, sun rufe babbar ƙofar makarantar domin hana zirga-zirgar ababen hawa saboda nuna adawa da ƙarin kuɗin makaranta da aka yi kwanan nan.

Kara karanta wannan

Karin Albashin N35k Da Jerin Tallafin Da Shugaba Tinubu Ya Fito Da Su Bayan Cire Tallafin Man Fetur

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jaridar The Nation ta rahoto cewa hukumar OAU ta sanar da ƙarin kuɗin makaranta a ranar 14 ga Satumba, 2023.

Idan dai ba a manta ba, shugaban ƙungiyar ɗaliban makarantar, Akinremi Ojo, ya ce ɗaliban makarantar na iya dakatar da komai a makarantar, idan har ba a sauya ƙarin kuɗin makarantar ba.

Ojo, wanda ya zanta da manema labarai a harabar jami'ar a ranar Litinin, 18 ga watan Satumba, 2023, ya ce mahukuntan hukumar sun yi shiru tun bayan da suka sanar da sabon tsarin biyan kuɗaɗen, cewar rahoton The Punch

Sai dai, ƙungiyar ɗalibai ta ƙasa (NANS) ta kuma buƙaci mahukuntan makarantar da su rage kuɗaɗen makarantar da kaso 50%.

Jaridar Vanguard ta ƙara da cewa, NANS ta yi Allah wadai da matakin da mahukuntan OAU suka ɗauka na ƙara kuɗin makaranta duk da umarnin da fadar shugaban ƙasa da majalisar wakilai suka bayar na hana yin hakan.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Sake Kai Sabon Hari a Arewacin Najeriya, Sun Sace Mutane Masu Yawa

LASU Ta Rage Kudin Makaranta

A wani labarin kuma, jami'ar jihar Legas (LASU) ta rage kuɗin makarantar da ta ƙara ga ɗaliban da ke karatu a cikinta.

Hukumar makarantar ta sanar da rage kuɗin makarantar ne bayan ta gana da ƙungiyar ɗalibai ta ƙasa (NANS).

Asali: Legit.ng

Online view pixel