Jam'iyyar APC Ta Yi Wa Atiku Da PDP Shagube Kan Takardun Karatun Tinubu a CSU

Jam'iyyar APC Ta Yi Wa Atiku Da PDP Shagube Kan Takardun Karatun Tinubu a CSU

  • Jam’iyyar APC ta yi wa jam’iyyar PDP da Atiku Abubakar, shuguɓe kan yadda suka yi ƙoƙarin samun takardun bayanan karatun Tinubu a jami'ar jihar Chicago
  • Bala Ibrahim, daraktan watsa labarai na jam'iyyar APC na ƙasa, ya ce Atiku da PDP na fama da cutar shan kayen da suka yi a zaɓen bana
  • A cewar Ibrahim, abu na gaba ga jam'iyyar PDP da Atiku shi ne shigar da ƙara kan ko sau nawa Tinubu ƴa shiga aji

FCT, Abuja - Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta caccaki Atiku Abubakar, ɗan takarar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaɓen shugaban ƙasa da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu, kan yadda ya bi diddigin karatun Shugaba Bola Tinubu a jami'ar jihar Chicago.

A cewar rahoton The Punch, jam'iyyar mai mulki ta ce jam'iyyar PDP da Atiku na fama cutar da shan kaye a zaɓen shugaban ƙasa na 2023, inda ta buƙaci tsohon mataimakin shugaban ƙasar da ya yi ritaya daga siyasa.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Kotu Ta Karanto Hukunci Kan Nasarar Gwamnan PDP, Ta Tabbatar da Wanda Ya Ci Zaɓe

APC ta caccaki PDP da Atiku
Jam'iyyar APC ta yi wa PDP da Atiku shaguɓe ka binciken bayanan karatun Tinubu Hoto: Bola Ahmed Tinubu, Atiku Abubakar
Asali: Twitter

APC ta yi martani kan yadda Atiku ya samu bayanan karatun Tinubu

Bala Ibrahim, daraktan watsa labarai na jam’iyyar APC na ƙasa, ya bayyana matakin da jam’iyyar PDP ta ɗauka a matsayin "cutar rashin nasara bayan zaɓe".

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Atiku ya samu nasarar fitar da bayanan karatun Shugaba Bola Tinubu daga jami’ar jihar Chicago biyo bayan bukatar hakan da ya yi daga jami'ar.

Da yake mayar da nasa martanin, Ibrahim ya caccaki jam'iyyar PDP saboda rashin amincewa da shan kaye a zaɓe, inda ya yi kira ga ɗan takararta na shugaban ƙasa da ya yi ritaya daga siyasa.

Cutar shan kaye na damun Atiku da PDP, cewar APC

Jigon na APC ya yi izgili da cewa nan ba da daɗewa ba Atiku da PDP za su sake shigar da kara a wata kotu a Amurka, inda za su nemi a ba su adadin lokutan da Shugaba Tinubu ya halarci azuzuwa a lokacin da yake karatun digiri.

Kara karanta wannan

Jami'ar Jihar Chicago: Peter Obi Ya Taso Tinubu a Gaba Kan Takardun Bayanan Karatunsa

A kalamansa:

"Mun sha faɗa sau da dama cewa PDP da Atiku suna fama da matsalar rashin lafiya. Abu na gaba da za su yi a yanzu shi ne su sake shigar da wata ƙara a kotu suna neman sau nawa Tinubu ya halarci lakcoci a jami'ar jihar Chicago."

Jami'ar Chicago Ta Ba Atiku Takardun Karatun Tinubu

A wani labarin kuma, jami'ar jihar Chicago (CSU), ta miƙa takardun karatun Shugaba Tinubu ga Atiku Abubakar.

Lauyoyin Atiku Abubakar su ne suka karɓi takardun karatun na Shugaba Tinubu biyo bayan umarnin da kotu ta yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel