Budurwa Ta Koma Cizon Yatsa Bayan Saurayin Da Taimaka Ya Koma Kasar Waje Ya Rabu Da Ita

Budurwa Ta Koma Cizon Yatsa Bayan Saurayin Da Taimaka Ya Koma Kasar Waje Ya Rabu Da Ita

  • Wata budurwa da ta yarda da soyayyar da take yi wa saurayinta, ta gamu da ɓacin rai bayan ya koma ƙasar waje
  • Budurwar ta ce duk da ta kashe ƴan kuɗaɗenta akan saurayin, ya manta da ita kuma ya ƙi cika alƙawari
  • A cewarta, a lokacin da take fuskantar kora daga gidan da take haya, saurayin yana can yana kashe maƙudan kuɗaɗe kan abokansa

Wata budurwa ƴar Najeriya ta yi nadamar matakin da ta ɗauka na tallafa wa masoyinta da ya yi balaguro zuwa ƙasar waje ya manta da ita duk da yadda ta tallafa masa.

Budurwar mai amfani da sunan (@proudlymotherof5) ta ce a ranar da zai tafi, ta kwashe kuɗaɗenta domin tabbatar da cewa ya sami dukkan abubuwan da yake buƙata.

Budurwa ta koka bayan saurayinta ya rabu da ita
Budurwar ta ce kudinta ta kwashe domin ya tafi kasar waje Hoto: @proudlymotherof5
Asali: TikTok

Ta ƙara da cewa tun daga lokacin ne saurayin ya yanke duk wata alaƙa tsakanin shi da ita, inda ya saɓa alƙawarin da ya yi na cewa ba zai manta da ita ba.

Kara karanta wannan

Gwamna Abba Gida-Gida Ya Tuna Da Dalibai Mata, Ya Yi Musu Wani Babban Gata

A wani faifan bidiyo, budurwar ta ce mutumin ya tallafa wa abokansa da N5m a lokacin da ta kasa samun kuɗin biyan hayar gida. Ta yi mamakin yadda ya sauya bayan ya samu kuɗi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kafin ya yi tafiya zuwa ƙasar waje, budurwar ta ce:

"Ya yi mini alƙawari a gaban teku a Legas, cewa zai saya mini gidan da nake so, mota, kasuwanci da biza, kuma idan ya rabu da ni zai yi rashin lafiya."

Ƴan soshiyal midiya sun yi martani

Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin martanin da aka yi a ƙasa:

@user4026669708117 ta rubuta:

"Da na kashe kuɗina akan saurayi gwara na yi amfani da kuɗin na siya akuya na tafi da ita ƙasar waje."

@Peace-Ougenwood ya rubuta:

"Abin da ya fi zafi a duniya shi ne cin amana, Chai, abin takaici."

Kara karanta wannan

Yadda Mahaifiya Ta Yi Ta Maza Ta Cafke Dan Ta'addan Da Ya Yi Garkuwa Tare Da Halaka Yarta

@Success ta rubuta:

"Waɗannan ƴan matan da ke ƙasashen waje suna aiki kuma suna samun kuɗi shi ya sa wasu mazan suke mantawa da ƴan matansu a Najeriya. Allah zai kawo miki mafita.

Yar Najeriya Ta Yi Wuff Da Bature

A wani labarin kuma, wata budurwa ƴar Najeriya ta cika da murna bayan ta yi wuff da wani dattijon bature.

Sai dai, masu amfani da yanar gizo sun yi mata ca kan cewa ta auri dattijon da ya girme ta nesa ba kusa ba, wanda hakan bai yi mata daɗi ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel