Manyan Labarai A Yau
Miyagun ƴan bindiga sun halaka mutum uku a wani sabon hari da suka kai a ƙaramar hukumar Logo ta jihar Benue. Al'ummar yankin sun buƙaci gwamnati ta kai musu ɗauki.
Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta samu koma baya a jihar Kaduna, bayan babban jigonta ya sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC mai mulki a Kaduna.
Sojojin ƙasar Isra'ila sun bayyana cewa sun halaka ɗaya daga cikin kwamandojin ƙungiyar Hamas ta ƙasar a Falasɗinu a wani hari ta sama da suka kai a zirin gaza.
Ƴan ta'addan mayaƙan ƙungiyar ISWAP sun sha kashin su a hannu bayan jiragen yaƙin dakarun sojin saman Najeriya sun yi musu luguden wuta jihar Borno.
Dakarun sojojin Najeriya na Operation Hadarin Daji sun samu nasarar ceto ɗaliban jami'ar gwamnatin tarayya Gusau (FUGUS) da ke jihar Zamfara da aka sace.
Rundunar ƴan sandan jihar Ogun ta tabbatar da cafke wasu ɓarayi da ake zargi da aikata laifin sace rawanin wani babban basaraken gargajiya a jihar Ogun.
Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya bayyana kuɗin fansan da ƴan bindiga suka ƙarba kafin su sako ɗaliban jami'ar jihar da suka yi awon gaba da su.
Ƴan bindiga sun sake kai farmaki cikin tsakar dare a jami'ar gwamnatin tarayya ta Gusau (FUGUS) da ke jihar Zamfara. Ƴan bindigan sun sace ɗalibai guda biyu.
Gambo Haruna, wata bazawara da mijinta ya mutu shekaru shida da suka gabata bayan fama da rashin lafiya, tana sana’ar tura baro domin ciyar da yaranta shida.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari