Hukumar NUC Ta Musanta Cire Bambancin da Ke Tsakanin Kwalin Digiri da HND

Hukumar NUC Ta Musanta Cire Bambancin da Ke Tsakanin Kwalin Digiri da HND

  • Hukumar kula da jami’o’i ta kasa (NUC) ta yi watsi da iƙirarin da ake na cewa an kawo karshen bambancin da ke tsakanin takardar kammala digiri da HND
  • Muƙaddashin sakataren NUC, Chris Maiyaki ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu bai amince da kudirin da zai kawo ƙarshen bambancin da ke tsakaninsu ba
  • A cewarsa, duk da cewa ana cigaba da kiraye-kiraye kuma majalisa ta amince da ƙudirin, amma babu wata doka da ta goyi bayansa a halin yanzu

FCT, AbujaHukumar kula da jami'o'i ta ƙasa (NUC) ta ce har yanzu akwai banbance-banbancen da ke tsakanin masu digiri na jami’a da masu kwalin babbar Diploma ta ƙasa (HND).

Hukumar ta ƙara da cewa har yanzu Tinubu bai sanya hannu kan dokar soke bambancin ba.

Kara karanta wannan

BBC Ta Tsaya Kan Bakanta Cewa Shugaba Tinubu Bai Yi Jabun Satikifet Na Jami'ar Chicago Ba

NUC ta yi magana kan cire bambancin da ke tsakanin digiri da HND
Hukumar NUC ta ce har yanzu akwai bambanci tsakanin digiri da HND Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Muƙaddashin sakataren NUC, Chris Maiyaki, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, 15 ga watan Oktoba, ya yi watsi da rahoton cewa hukumar kula da ilimin fasaha ta ƙasa (NBTE) ta fara bayar da kwas na shekara ɗaya domin ganin HND ya daidaita da digiri, Daily Independent ta ruwaito.

A cewar Maiyaki, hankalin hukumar NUC ya karkata kan labarin cewa hukumar NBTE ta ɓullo da shirin kammala karatun digiri na tsawon shekara ɗaya a kwalejojin fasaha na Najeriya a hukumance domin ba masu kwalin HND damar sauya kwalinsu zuwa digiri.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Har yanzu akwai bambanci a tsakanin digiri da HND

Ya ƙara da cewa, labaran da aka samu ta yanar gizo an ce sun fito ne daga Farfesa Idirs Bugaje, babban sakataren NBTE, da Fatima Abubakar, shugabar sashen yaɗa labarai na hukumar, amma rahoton ba gaskiya ba ne.

Kara karanta wannan

Ministan Birnin Tarayya Nyesom Wike Ya Bayyana Dalilin da Yasa Ya Yarda Ya Yi Aiki da Tinubu

Shugaban na NUC ya cigaba da cewa, rahoton ya ce sun ɗauki matakin ne saboda kiraye-kirayen da ake yi na a cire bambancin da ke tsakanin masu digiri da masu HND a wuraren aikinsu.

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

"Duk da cewa ana ci gaba da tada jijiyoyin wuya na ganin an kawar da bambancin da ke tsakanin digiri da HND, har ya zuwa yanzu babu wata doka da ta kawar da bambancin da ke tsakaninsu."

NECO Ta Saki Sakamakon Jarabawa

A wani labarin kuma, hukumar shirya jarabawa ta ƙasa (NECO) ta saki sakamakon jarabawar SSCE na shekarar 2023.

Hukumar ta bayyana cewa a sakamakon na bana, kaso 61.60% cikin 100 na ɗaliban da suka zana jarabawar, sun samu kiredit biyar ciki har da lissafi da Ingilishi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel