Yan Bindiga Sun Halaka Mutum 3 a Wani Sabon Hari a Benue

Yan Bindiga Sun Halaka Mutum 3 a Wani Sabon Hari a Benue

  • Ƴan bindiga ɗauke da makamai sun kai sabon harin ta'addanci a ƙaramar hukumar Logo ta jihar Benue
  • Harin wanda ƴan bindigan suka kai a ƙauyen Imaton na ƙaramar hukumar ya salwantar da rayukan mutum uku
  • Mutanen yankin sun koka kan yadda ake yawan kai musu hare-hare inda suka buƙaci gwamnati da ta kawo musu ɗauki

Jihar Benue - Ƴan bindiga sun halaka mutum uku a wani sabon hari da suka kai a dandalin ƙauyen Imaton da ke unguwar Ukemberagya a cikin Gaambe-Tiev na ƙaramar hukumar Logo ta jihar Benue.

Mazauna yankin sun ce lamarin ya faru ne da karfe 9:00 na daren ranar Asabar, 14 ga watan Oktoban 2023, cewar rahoton Daily Trust.

Yan bindiga sun halaka mutum uku a Benue
Yan bindiga sun salwantar da rayukan mutum uku a Benue Hoto: Theguardian.com
Asali: UGC

Sun lissafo sunayen matasa uku da maharan ɗauke da makamai suka kashe a matsayin, Tertsea Terkimbi, Tertsea Mkposu da Mimi Umburga.

Kara karanta wannan

Barayi Sun Kutsa Fadar Babban Basarake, Sun Tafka Gagarumar Ta'asa

Wani shugaban al'ummar yankin, Cif Joseph Anawah, ya bayyana cewa baya ga abin da ya faru a ranar Asabar, an kai musu hare-hare cikin watanni biyu da suka gabata, rahoton Punch ya tabbatar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Anawah ya ce, sabbin hare-haren da ƴan bindigan ke kai wa kan al'ummar Gaambe-Tiev musamman na ƙauyen Ukemberagya da ke ƙaramar hukumar Logo ta jihar ya dauki wani salo na daban mai ban tsoro.

Al'ummar yankin sun koka

Ya koka cewa waɗannan sabbin hare-haren da kashe-kashen, ana yin su ne da nufin korar manoman yankin ta yadda shanu za su cinye amfanin gonan da ba a girbe ba.

Anawah ya yi kira ga gwamnatin jiha da ta tarayya da su gaggauta tura jami’an tsaro domin tabbatar da tsaro a yankin, yana mai jaddada cewa idan har aka samar da tsaro a ƙauyukan Chembe da unguwar Iorza da kuma ƙauyen Jootar, zai taimaka matuka wajen samar da tsaro ga jama’a.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Yan Bindiga Sun Sake Sace Dalibai a Jami'ar Gwamnatin Tarayya Da Ke Gusau, Bayanai Sun Fito

Wane martani ƴan sanda suka yi?

Lokacin da aka tuntuɓi kakakin rundunar ƴan sandan jihar, SP Catherine Anene, kan abin da ya faru a yankin, ta bayyana cewa ba ta samu wani labari ba daga ƙaramar hukumar Logo.

Sojoji Sun Sheke Mayakan ISWAP

A wani labarin kuma, jiragen yaƙin rundunar sojin saman Najeriya sun yi luguden wuta kan mayaƙan ƙungiyar ISWAP a jihar Borno.

Harin da sojojin suka kai kan ƴan ta'addan lokacin da suke gudanar da taro, ya yi sanadiyyar halaka aƙalla mutum 100 daga cikinsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel