Dakarun Sojojin Sama Sun Halaka Mayakan ISWAP 100 a Jihar Borno

Dakarun Sojojin Sama Sun Halaka Mayakan ISWAP 100 a Jihar Borno

  • Jiragen yaƙin rundunar sojojin saman Najeriya sun halaka mayaƙan ƙungiyar ƴan ta'addan ISWAP a wani sabon hari a jihar Borno
  • Jiragen yaƙin sun farmaki ƴan ta'addan ne bayan sun taru domin kitsa yadda za su kai hare-haren ta'addanci kan jami'an tsaro
  • Harin na dakarun sojojin ya yi sanadiyyar halaka mayaƙan na ƙungiyar ISWAP kusan aƙalla mutum 100

Jihar Borno - Aƙalla sama da mutum 100 da ake zargin mayaƙan ƙungiyar ISWAP ne suka halaka a wani hari da jiragen yaƙin rundunar haɗin gwiwa ta Operation Hadin Kai a yankin Arewa maso gabas suka kai a jihar Borno.

Jiragen yaƙin na rundunar sojojin saman sun kai harin ne a ranar Juma'a, 13 ga watan Oktoban 2023.

Jiragen yaki sun halaka mayakan ISWAP
Dakarun sojojin sama sun halaka mayakan ISWAP 100 Hoto: Nigerian Airforce
Asali: Twitter

A cewar Zagazola Makama, wani masani kan harkokin tsaro a yankin tafkin Chadi, an kai harin ne a lokacin da ƴan ta'addan ke ganawa a dajin Bukar Mairam a ƙaramar hukumar Marte ta jihar Borno.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Dakarun Sojoji Sun Ceto Daliban Jami'ar FUGUS, Bayanai Sun Bayyana

Yadda aka kai harin

Zagazola ya ce an kai harin ta sama ne biyo bayan binciken da aka gudanar wanda ya nuna ƴan ta'adda na taro a yankin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani majiyar soji ya bayyana cewa:

"Kayayyakin leƙen sirri na ISR sun hango wani gagarumin yunƙuri na ƴan ta'adda masu tayar da ƙayar baya na tafiya zuwa wani wuri da ake zargin cewa dandalin haduwar ƴan ta'addan ne."
"Hare-haren sun yi nasara, inda suka yi gagarumar ɓarna a wurin da ƴan ta'addan su ke."
"Yan ta'addan sun taru a wurin ne domin shirya kai hare-hare da daddare a kan wuraren da sojojinmu suke."

A makon da ya gabata, wani harin da sojojin saman Najeriya suka kai ta sama, ya kashe ƴan bindiga sama da 100 a jihar Kebbi.

Sojoji Sun Ceto Daliban FUGUS da Aka Sace

Kara karanta wannan

Barayi Sun Kutsa Fadar Babban Basarake, Sun Tafka Gagarumar Ta'asa

A wani labarin kuma, dakarun sojojin Najeriya na Operation Hadarin Daji sun samu nasarar ceto ɗaliban jami'ar FUGUS da ƴan bindiga suka sace.

Dakarun sojojin sun ceto ɗaliban ne bayan sun yi musayar wita da ƴan bindigan da suka sace su a ranar Asabar, 24 ga watan Oktoban 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng