Shugaba Tinubu Ya Kaddamar da Tallafin Kudi Ga Gidaje Miliyan 15

Shugaba Tinubu Ya Kaddamar da Tallafin Kudi Ga Gidaje Miliyan 15

  • Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ƙaddamar da shirin rabon tallafin kuɗi ga gidaje miliyan 15 domin rage musu raɗaɗi
  • Sabon shirin rabon tallafin kuɗaɗen dai zai amfani ƴan Najeriya miliyan 62 waɗanda ke fama da matsanancin talauci
  • Sakataren gwamnatin tarayya, George Akume shi ne ya wakilci Shugaba Tinubu wajen ƙaddamar da shirin da aka yi a ranar Talata, 17 ga watan Oktoba

FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ƙaddamar da shirin rabon tallafin kuɗi ga gidaje miliyan 15.

Jaridar Channels tv ta kawo rahoto cewa taron ƙaddamar da shirin ya gudana ne a ɗakin taro na ƴan jarida na gidan gwamnati da ke Abuja, a ranar Talata, 17 ga watan Oktoban 2023.

Shugaba Tinubu ya kaddamar da tallafin rabon kudi
Shugaba Tinubu ya kaddamar da tallafin rabon kudi ga gidaje miliyan 15 Hoto: @OfficialABAT
Asali: Twitter

Sakataren gwamnatin tarayya, George Akume, shi ne ya wakilci Shugaba Tinubu a wajen taron wanda ya zo daidai da ranar yaƙi da fatara ta duniya.

Kara karanta wannan

Gwammatin Tinubu Ta Buɗe Shafin Ɗaukar Mutane Aikin N-Power Na 2023? Gaskiya Ta Bayyana

Tinubu ya sanar da shirin bayar da tallafin kuɗin ne a lokacin da ya gabatar da jawabin ranar samun ƴancin kai ga ƴan Najeriya a ranar 1 ga Oktoban 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan Najeriya nawa ne za su amfana?

Ministar agaji da kawar da talauci, Betta Edu, ta ce gidaje miliyan 15 ɗin suna wakiltar ƴan Najeriya miliyan 62.

A cewar Edu, Naira 25,000 za a riƙa ba wadanda suka amfana da shirin a kowane wata har na tsawon watanni uku, rahoton Vanguard ya tabbatar.

Ministan ta ƙara da cewa za a kaddamar da wani sabon shiri mai suna ‘Iya Loja Funds’ domin bayar da lamuni mai sauƙi na N50,000 domin tallafa wa ƙananan ƴan kasuwa.

A wajen rabon kuɗin ga waɗanda za su amfana da shirin, ministan kuɗi, Wale Edun, ya bayyana cewa za a samar da tsarin tantance wa na amfani da bayana ƴan yatsu domin tabbatar da gaskiya da bin diddigi.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu Zai Gabatar da Kasafin Kuɗin 2024 Wanda Ya Haura N20tr, Bayanai Sun Fito

Sabon Tallafin Tinubu Ga Dalibai

A wani labarin kuma, shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sanar da sabon tallafi ga ɗaliban Najeriya da ke karatu a makarantun gaba da sakandare.

Shugaban ƙasar ya bada umarnin raba motocin Bas-Bas ga jami'o'i, kwalejojin fasa da kwalin ilimin da ke sassan ƙasar nan baki ɗaya, domin sauƙaƙawa ɗalibai wajen zirga-zirga.

Asali: Legit.ng

Online view pixel