Sojojin Isra'ila Sun Ce Sun Halaka Kwamandan Kungiyar Hamas a Gaza

Sojojin Isra'ila Sun Ce Sun Halaka Kwamandan Kungiyar Hamas a Gaza

  • Dakarun tsaron ƙasar Isra'ila (IDF) sun bayyana cewa sun halaka ɗaya daga cikin kwamandojin ƙungiyar Hamas a zirin Gaza
  • Dakarun na IDF sun bayyana cewa sun halaka kwamandan ne wanda yana ɗaya daga cikin waɗanda suka shirya harin da ƙungiyar Hamas ta kai musu
  • Ƙasar Isra'ila na cigaba da kai hare-hare ta sama a zirin Gaza domin ramuwar gayya kan harin da Hamas ta kai mata

Isra'ila - Dakarun tsaron Isra'ila sun ce sun kashe wani mutum a zirin Gaza da ake zargin yana ɗaya daga cikin kwamandojin ƙungiyar Hamas da suka shirya manyan hare-haren da ƙungiyar ta kai a ƙasar Isra'ila.

Sanarwar da rundunar ta fitar a ranar Lahadi, 15 ga watan Oktoban 2023, ta bayyana cewa, an kashe kwamandan rundunan Hamas ɗin ne mai sun Bilal Al Kedra, a Kudancin Khan Younis, a wani harin da aka kai ta sama a yammacin ranar Asabar.

Kara karanta wannan

Dakarun Sojoji Sun Samu Nasara Kan Yan Bindiga, Sun Ceto Mutane da Dama da Suka Sace a Arewacin Najeriya

Sojojin Isra'ila sun halaka kwamandan Hamas
Ana cigaba da gwabza fada tsakanin Hamas da Isra'ila
Asali: Twitter

Rundunar sojin ta IDF ta kuma bayyana cewa ta halaka wasu mayaƙan ƙungiyar ta Hamas, cewar rahoton Times of India.

Isra'ila na cigaba da kai hare-hare a zirin Gaza

Labarin baya-bayan nan ya zo ne bayan da IDF ta ce ta kashe wasu mutum biyu da take zargi da kitsa hare-haren da ƙungiyar Hamas ta kai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rundunar ta IDF ta kai hari sama da wurare 100 na sojojin Hamas a Zeitoun, Khan Younis, da Yammacin Jabalia, in ji ta, inda suka kai hari kan wuraren bayar da umarni, wuraren soji da wuraren harba makami mai linzami.

Rundunar ta IDF ta ce kai hari kan cibiyoyin bayar da umarni na ƙungiyar ta Hamas da dama.

Ƙungiyar EU da Amurka da Isra'ila sun ayyana Hamas a matsayin ƙungiyar ta'addanci.

Sai dai, ƙungiyar tana fafutuka ne kan samar da ƴancin Falasɗinawa bisa mamayar da ƙasar Isra'ila ta kwashe shekaru masu yawa tana yi musu.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Hankula Sun Tashi Yayin Da Sojojin Isra'ila Suka Kutsa Cikin Zirin Gaza

Sojojin Isra'ila Sun Kutsa Zirin Gaza

A wani labarin kuma, Falasɗinawa da dama sun fara ficewa daga gidajensu domin tsira da rayukansu, yayin da sojojin Isra'ila suka kutsa cikin zirin Gaza.

Sojojin na ƙasar Isra'ila sun kutsa zirin Gaza ne a cigaba da faɗan da suke yi da ƙungiyar Hamas mai kare Falasɗinawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel