Jami'ar Tehran Ta Karrama Sheikh Zakzaky Da Digirin Girmamawa

Jami'ar Tehran Ta Karrama Sheikh Zakzaky Da Digirin Girmamawa

  • Jagoran mabiya ƙungiyar Shi'a a Najeriya, Sheikh Ibraheem El-Zakzaky ya samu digirin digir-gir daga jami'ar Tehran ta ƙasar Iran
  • Jami'ar Tehran ta karrama jagoran na mabiya Shi'a ne a wani taron yaye ɗalibanta da ta gudanar a ranar Asabar, 14 ga watan Oktoban 2023
  • Jami'ar Tehran na ɗaya daga cikin jami'o'in da ake ji da su a ƙasar Iran da yankin nahiyar Asiya gaba ɗaya

Kasar Iran - Jagoran mabiya Shi'a na Najeriya a ƙarƙashin ƙungiyar Islamic Movement of Nigeria (IMN), Sheikh Ibraheem El-Zakzaky ya samu karramawa ta digirin girmamawa daga jami'ar Tehran ta ƙasar Iran.

A cewar wata sanarwa da Dakta Fatima Ismaeel Hassan ƴar kungiyar ta IMN ta fitar, an karrama Zakzaky ne a wajen wani taron yaye ɗalibai da jami'ar ta shirya a ranar Asabar, 14 ga watan Oktoban 2023, cewar rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Innalillahi: 'Yan Arewa sun shiga jimami bayan mutuwar mahaifiyar tsohon shugaban majalisa

Zakzaky ya samu digirin digir-gir
Jami'ar Tehran ta karrama Sheikh Zakzaky da digirin digir-gir Hoto: IRNA
Asali: Facebook

Meyasa jami'ar ta karrama Sheikh Zakzaky?

Hassan ta ambato jami'ar na cewa an bayar da wannan karramawar ne sakamakon amincewar da majalisar zartaswar jami'ar ta yi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Bayan nazari kan rayuwa, ilimi da gwagwarmayar Shehin malamin, majalisar zartaswar jami'ar baki ɗaya ta amince da baiwa Sheikh Ibraheem Ya’qoub El-Zakzaky (H) lambar yabo ta digirin digir-gir na girmamawa (Honoris Causa) a fannin Ilimin Duniya: zaman lafiya da magance rikici."

Jami'ar Tehran tana cikin manyan jami'o'i 500 a duniya. A cewar cibiyar ƙididdigar jami'o'i ta duniya, jami'ar Tehran ta kasance ta biyu a Iran, ta 157 a yankin Asiya, sannan ta 495 a duniya.

Wani ɓangare na sanarwar da Dr Fatima ta fitar na cewa:

"Yayin da muke taya shugabanmu murnar wannan karramawa, muna kira ga mutane da su yi gwagwarmayar ƴantar da ƴan Adam daga bauta, azzalumai, da rashin adalci."

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Babban Jami'in PDP Na Kasa Ya Koma APC, Bayanai Sun Bayyana

Yan Shi'a Sun Yi Tattakin Goyon Baya Ga Falasdinu

A wani labarin kuma, mabiya ƙungiyar Shi'a a Najeriya sun fito domin nuna goyon bayansu ga al'ummar Falasɗinawa biyo bayan ɓarkewar sabon rikici tsakaninsu da ƙasar Isra'ila.

Tawagar mabiya aƙidar ta Shi'a sun gudanar da tattakin na nuna goyon baya ga Falasɗinawa a birnin Tarayya Abuja, a ranar Litinin, 9 ga watan Oktoban 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel