Yan Bindiga Sun Sake Sace Dalibai a Jami'ar Gwamnatin Tarayya Ta Gusau

Yan Bindiga Sun Sake Sace Dalibai a Jami'ar Gwamnatin Tarayya Ta Gusau

  • Ƴan bindiga sun sake kai farmaki a jami'ar gwamnatin tarayya ta Gusau (FUGUS) da ke jihar Zamfara, a daren ranar Asabar, 14 ga watan Oktoba
  • Miyagun ƴan bindigan sun yi awon gaba da wssu ɗalibai guda biyu na jami'ar a sabon farmakin da suka kawo
  • Jami'an tsaro sun bi sahun ƴan bindigan domin tabbatar da cewa sun ceto ɗaliban da suka sace zuwa cikin daji

Jihar Zamfara - Wasu ƴan bindiga a yammacin ranar Asabar, 14 ga watan Oktoba, sun sake yin garkuwa da wasu ɗaliban jami'ar tarayya ta Gusau (FUGUS) da ke jihar Zamfara, cewar rahoton jaridar Channels tv.

A cewar shaidar ganau ba jiyau ba, ɗaliban guda biyu waɗanda namiji da mace ne, an sace su a ɗakin kwanan ɗaliban da ke kusa da jami'ar da misalin karfe 9:00 na daren ranar Asabar a unguwar Sabon Garin Damba da ke Gusau, babban birnin jihar.

Kara karanta wannan

'Dalibai Mata Na Jami'ar Arewa da 'Yan Bindiga Suka Sace Sun Shaƙi Iskar 'Yanci, Bayanai Sun Fito

Yan bindiga sun sace dalibai a FUGUS
Yan bindiga sun kara sace dalibai a jami'ar FUGUS Hoto: Dauda Lawal
Asali: Facebook

Mazauna yankin sun ce ƴan bindigan sun farmaki unguwar ne ƴan mintuna kaɗan bayan karfe 8:00 na dare inda suka yi ta harbin kan mai uwa da wabi domin tsorata mazauna yankin.

Wane ƙoƙari jami'an tsaro suka yi?

Jami’an tsaro sun yi ta musayar wuta da ƴan ta'addan a ƙoƙarin fatattakarsu, amma ƴan ta'addan sun tafi da ɗalibai guda biyu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani mazaunin unguwar da ya nemi a sakaya sunansa saboda dalilai na tsaro ya bayyana cewa jami'an tsaro na haɗin gwiwar ƴan sanda da sojoji, sun bi sahun ƴan ta'addan.

Kokarin yin magana da kakakin rundunar ƴan sandan jihar, ASP Yazid Abubakar, ya ci tura domin bai amsa kiran da aka yi masa a waya.

Sake sace ɗaliban na zuwa ne bayan a kwanakin baya ƴan bindigan sun sace ɗaliban makarantar mata, a ranar 22 ga watan Satumban 2023.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Gindaya Sharaɗi Kafin Su Sako Ɗalibai Mata da Suka Sace a Jami'ar Arewa

Ba Batun Sulhu da Yan Bindiga a Zamfara

A wani labarin kuma, gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal Dare, ya nanata kuɗirinsa na cewa gwamnatinsa ba za ta tattauna da ƴan bindiga ba domin kawo ƙarshen matsalar tsaro a jihar.

Gwamnan ya yi nuni da cewa ƴan bindigan ba su san darajar ran ɗan Adam ba, kuma ba su mutunta alƙawari domin gwamnatocin baya sun yi sulhu da su, amma hakan bai haifar da ɗa mai ido ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel