Manyan Labarai A Yau
An kwashi Joe Ajaero, shugaban kungiyar kwadago na kasa (NLC) zuwa wani asibiti a Owerri, babban birnin jihar Imo inda yake samun kulawar likitoci.
Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike ya yi bayanin cewa ba zai bari Sim Fubara ya yi aiki da makiyansa ba bayan ya yi aiki don ganin ya zama gwamnan Ribas.
Babban bankin Najeriya (CBN) ya yi magana kan lokacin da za a daina amfani da tsofaffin takardun kuɗi, a yayin da wa'adin ranar 31, ga watan Disamba ya matso.
Wata babbar kotu a jihar Ribas ta hana majalisar dokokin jihar tsige Gwamna Siminalayi Fubara. An dai samu rikicin siyasa a jihar Rivers cikin kwanakin nan.
A ranar Laraba, majalisar dattawan Najeriya ta amince da dala biliyan 7.8 da kuma yuro miliyan 100 a matsayin kudin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai ciyo bashi.
Wani mutumi da ya dawo daga gidan yari bayan shekaru 15 ya tambayi dalilin da yasa bai ga kowa ba a dandalin 2go. Bidiyon ya yadu a soshiyal midiya.
Kotun ɗaukaka ƙara ta ƙwace kujerar sanatan Benue ta Arewa maso Gabas daga hannun Sanata Gabriel Suswam, ta tabbatar da nasarar ɗan takarar jam'iyyar APC.
Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Rivers, ya yi magana kan rashin jituwarsa da tsohon gwamnan jihar kuma ministan birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike.
An samu asarar rayukan mutum 12, yayin da wata motar bas da suke ciki ta yi taho mu gama da wata babbar mota ƙirar Toyota Canter a jihar Zamfara.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari