Bayan Naira Triliyan 2.17, Majalisar Dattawa Ta Lamuncewa Tinubu Ciyo Bashin $7.8Bn da €100M

Bayan Naira Triliyan 2.17, Majalisar Dattawa Ta Lamuncewa Tinubu Ciyo Bashin $7.8Bn da €100M

  • An amince da bukatar gwamnatin tarayya karkashin jagorancin Shugaban kasa Tinubu na ciyo bashi
  • A zamanta na ranar Laraba, 1 ga watan Nuwamba, majalisar dattawa ta amince da bukatar Tinubu na ciyo bashin dala biliyan 7.8 da Yuro miliyan 100
  • Hakan na zuwa ne kwana daya bayan Shugaban kasar ya nemi majalisar da ta amince da naira tiriliyan 2.17 a matsayin karin kasafin kudin 2023

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Abuja - Majalisar dattawa ta amince da bukatar shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu na ciyo bashin dala biliyan 7.7 da Yuro miliyan 100 a ranar Laraba, 1 ga watan Nuwamba.

Majalisar dattawa ta amince Tinubu ya ciyo bashi
Bayan Naira Triliyan 2.17, Majalisar Dattawa Ta Lamuncewa Tinubu Ciyo Bashin $7.8Bn da €100M Hoto: The Senate President - Nigeria, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Dalilin da yasa Tinubu yake neman ciyo bashin $7.8Bn da €100M

Kara karanta wannan

Tinubu zai kashe Naira Biliyan 1.5 wajen sayo motocin uwargidar Shugaban kasa

Shugaban kasar ya aika wasika zuwa majalisar dattawa yana neman ta duba tare da amince da tsarin rance na 2022 zuwa 2024 don kammala wasu ayyuka, Channels TV ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan na zuwa ne kwanaki biyu bayan majalisar zartarwa ta amince da naira tiriliyan 2.17 a matsayin karin kasafin kudin 2023, rahoton Vanguard.

Businessday ta rahoto cewa shirin da aka gabatar na neman ciyo bashin dala biliyan 7.8 da kuma Yuro miliyan 100 don gudanar da ayyuka da shirye-shirye daban-daban a fadin bangarorin tattalin arzikin kasar.

Ayyukan sun hada da samar da ababen more rayuwa, noma, tsaro, samar da ayyukan yi, kiwon lafiya da dai sauransu.

Shugaban kasar ya kuma bayyana cewa bankin duniya ya nuna sha'awar bayar da tallafin kudi na dala biliyan 1 da dala biliyan 2 domin dakile tabarbarewar tattalin arziki da sauye-sauyen baya-bayan nan a kasar.

Kara karanta wannan

Magana ta fito: Manyan abubuwa 2 da suka haddasa rigima tsakanin Wike da Gwamna Fubara

Akpabio ya amince da bukatar Tinubu yayin zaman majalisa na ranar Laraba sannan ya mika shirin ga kwamitin kula da harkokin kudin waje, da tsare-tsare na kasa don ci gaba da tattaunawa.

Masu zanga-zanga na so a tsige minista

A wani labarin, daruruwan masu fafutukar tabbatar da dimokuradiyya a Najeriya sun fita tattaki da zanga-zangar lumana zuwa majalisar tarayya da ke Abuja ranar Laraba.

Masu zanga-zangar sun nemi a gaggauta tsige ƙaramin ministan tsaron Najeriya kuma tsohon gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel