Kotu Ta Kwace Kujerar Sanatan PDP, Ta Tabbatar da Dan Takarar APC a Matsayin Wanda Ya Lashe Zabe

Kotu Ta Kwace Kujerar Sanatan PDP, Ta Tabbatar da Dan Takarar APC a Matsayin Wanda Ya Lashe Zabe

  • Kotun ɗaukaka ƙara ta raba gardama kan taƙaddamar kujerar sanatan Benue ta Arewa maso Gabas
  • Kotun ta soke nasarar da Sanata Gabriel Suswam ya samu a kotun zaɓe wacce ta bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaɓen
  • Kotun ɗaukaka ƙarar ta tabbatar da Emmanuel Udende na jam'iyyar APC a matsayin sahihin wanda ya lashe zaɓen

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wakilin Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar fiye da shekara biyar wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum da nishaɗi

FCT, Abuja - Kotun ɗaukaka ƙara ta ƙwace kujerar sanatan Benue ta Arewa maso Gabas daga hannun Gabriel Suswam, na jam'iyyar PDP, inda ta miƙa ta a hannun ɗan takarar jam'iyyar APC.

A wani hukuncin bai ɗaya a ranar Laraba, 1 ga watan Nuwamban 2023, kotun mai alƙalai uku ta yi hukuncin cewa Gabriel Suswam ba shi ne ainihin wanda ya lashe zaɓen na ranar 25, ga watan Fabrairu ba, cewar rahoton The Nation.

Kara karanta wannan

Zaben gwamnan Bayelsa: Kotun daukaka kara ta yi hukunci kan matsayin takarar Timipre Sylva na APC

Kotu ta kwace kujerar Gabriel Suswam
Kotun daukaka kara ta kwace kujerar Sanata Gabriel Suswam Hoto: Gabriel Torwua Suswam
Asali: Facebook

Kotun daukaka ƙarar ta warware hukuncin da kotun zaɓe ta yi na tabbatar da Suswam a matsayin wanda ya lashe zaɓen tare da soke takardar shaidar cin zaɓen da INEC ta ba Emmanuel Udende na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kotun daukaka ƙarar ta soke takardar shaidar cin zaɓe da aka baiwa Suswam sannan ta umurci INEC da ta ba Udende sabuwar takardar shaidar cin zaɓe.

Meyasa kotun ta ƙwace kujerar Suswam?

Ta ce kotun ba ta tantance shaidun da ɓangarorin suka gabatar a gabanta yadda ya kamata ba, yayin da take sauraren ƙarar da Suswam ya shigar, inda ta kai ga cimma hukunci na kuskure da ta amince da ƙarar, wacce ta ƙalubalanci nasarar zaɓen Udende.

Kotun ta amince da ɗaukaka ƙarar da Udende ya yi, sannan ta warware hukuncin kotun zaɓen.

Kara karanta wannan

Da ɗumi-dumi: "Ba Tinubu ne ya lashe zaɓen shugaban ƙasa ba" Atiku Abubakar ya yi bayani

Mai shari’a Abimbola Obaseki-Adejumo, wanda ya karanta hukuncin, ya bayyana cewa:

"An warware hukuncin da kotun zaɓe ta yanke a ranar 8 ga watan Satumba."
"An tabbatar da wanda ya ɗaukaka ƙara a matsayin wanda ya lashe zaɓen sanatan Benue ta Arewa maso Gabas wanda aka gudanar a ranar 25, ga watan Fabrairu."

Kotu Ta Tsige Kakakin Majalisar Dokoki

A wani labarin kuma, kotun zaɓen ƴan majalisu a mai zamanta a Jos ta tsige kakakin majalisar dokokin jihar Plateau, Hon. Moses Sule.

Kotun ta ayyana tsohon shugaban masu rinjaye a majalisar, Hon. Naanlong Daniel a matsayin wanda ya lashe zaɓen.

Asali: Legit.ng

Online view pixel