Tashin Hankali Yayin da Aka Kwashi Shugaban NLC Ajaero Zuwa Asibiti, Cikakken Bayani

Tashin Hankali Yayin da Aka Kwashi Shugaban NLC Ajaero Zuwa Asibiti, Cikakken Bayani

  • Zanga-zangar da kungiyar kwadago ta kasa (NLC), reshen jihar Imo ta shirya ya hadu da gagarumin cikas a ranar Laraba, 1 ga watan Nuwamba
  • Lamarin ya yi sanadiyar kwantar da shugaban kungiyar na kasa, Joe Ajaero a asibiti
  • NLC dai kungiya ce ta kwadago wacce ke ingantawa tare da kare yancin al'ummar kasar musamman ma'aikata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Jihar Imo - Rahotanni sun kawo cewa an kwashi shugaban kungiyar kwadago ta kasa (NLC), Kwamrad Joe Ajaero zuwa wani asibiti a Owerri a ranar Laraba, 1 ga watan Nuwamba, inda yake samun kulawar likitoci.

Kamar yadda jaridar The Nation ta rahoto, shugaban sashin labarai na NLC, Kwamrad Benson Upah, ya bayyana cewa idon Ajaero na dama ya rufe ruf.

An kwashi shugaban NLC zuwa asibiti
Tashin Hankali Yayin da Aka Kwashi Shugaban NLC Ajaero Zuwa Asibiti, Cikakken Bayani Hoto: @NLCHeadquarters
Asali: Twitter

An ci zarafin shugaban NLC sosai, inji kungiyar

Kara karanta wannan

Kotu ta shiga tsakani, ta yanke hukunci kan yunkurin tsige gwamnan PDP

A ranar Laraba ne wasu jami'an tsaro dauke da makamai sun yi awon gaba da Ajaero a wajen zanga-zangar NLC a jihar Imo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Channels TV ta nakalto Upah yana cewa:

"An ji daga shugaban kungiyar kwadago, Kwamrad Joe Ajaero a yammacin nan da misalin karfe 3:30 na yamma a asibitin yan sanda da ke Owerri daga inda aka dauke shi zuwa asibitin tarayya ta Owerri inda yake samun kulawar likitoci.
"An ci zarafinsa sosai, idonsa na dama a rufe yake ruf a daidai lokacin da aka ji daga gare shi."

A halin da ake ciki, kungiyar ta ce idan har gwamnati ba ta saki Ajaero za ta durkusar da kasar da yajin aikin gama-gari.

Kungiyar ta ce daga yanzu zuwa karfe 12 na dare idan har ba ta samu abin da ta ke so ba, komai na iya faruwa a kasar.

Kara karanta wannan

Kama Daliban Jami’ar OAU: Zanga-zanga ta barke a ofishin EFCC

Yan sanda sun kama shugaban NLC

A baya Legit Hausa ta rahoto cewa jami'an tsaro sun kama shugaban Kungiyar Kwadago (NLC), Joe Ajaero a Owerri babban birnin jihar Imo.

Daruruwan jami'an 'yan sanda dauke da makamai sun kama Ajaero ne a sakatariyar kungiyar inda su ka tafi da shi.

Daraktan yada labarai na kungiyar, Benson Upper shi ya bayyana haka ga gidan talabijin na Channels. Ya ce lamarin ya faru ne a yau Laraba 1 ga watan Nuwamba a birnin Owerri da ke jihar Imo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel