Babban Bankin Najeriya CBN Ya Bayyana Lokacin da Za a Daina Amfani da Tsofaffin Takardun Kudi

Babban Bankin Najeriya CBN Ya Bayyana Lokacin da Za a Daina Amfani da Tsofaffin Takardun Kudi

  • Babban bankin Najeriya (CBN) ya yi magana kan wa'adin daina amfani da tsofaffin takardun kuɗi da yake ƙara gabatowa
  • Wani jami'in bankin ya bayyana cewa ba za a daina amfani da tsofaffin takardun kuɗaɗen ba ko da wa'adin ya cika
  • Jami'in ya yi nuni da cewa bankin a hankali zai janye tsofaffin takardun kuɗaɗen domin gudun a sake jefa ƴan Najeriya cikin wahala

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wakilin Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar fiye da shekara biyar wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum da nishaɗi

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya ce har yanzu takardun tsofaffin kuɗi na N200, N500 da N1000 za su cigaba da zama a matsayin halastattun kuɗi har bayan ranar 31, ga watan Disamban 2023.

Idan dai ba a manta ba a watan Maris ne babban bankin CBN ya sanar da cewa, bisa bin umarnin hukuncin da kotun ƙoli ta yanke, tsofaffin takardun kuɗin za su daina aiki a ranar 31, ga watan Disamba.

Kara karanta wannan

Hajjin 2024: An bayyana kudin da maniyyata ka iya biya domin zuwa Saudiyya

CBN ba zai janye tsofaffin takardun kudi a Disamba ba
CBN ya ce za a cigaba da amfani da tsofaffin kudi har bayan watan Disamba Hoto: Yemi Cardoso/George Osodi
Asali: UGC

A watan Oktoban shekarar da ta gabata ne tsohon gwamnan CBN, Godwin Emefiele, ya ƙaddamar da shirin sake fasalin takardun kuɗi na N200, N500 da N1,000, sannan ya buƙaci ƴan Najeriya da su kai tsofaffin takardun kuɗinsu bankuna kafin ranar 31, ga watan Janairun 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Umarnin Emefiele ya haifar da ƙarancin kuɗi a faɗin ƙasar nan a cikin watan Fabrairu, lamarin da ya jefa ƴan Najeriya cikin wahalhalu, wanda a ƙarshe ya haifar da zanga-zanga da kai hare-hare a kan bankuna a wasu garuruwa.

Yaushe CBN zai janye tsofaffin kuɗi?

A halin da ake ciki, a yayin da ƙarancin takardun kuɗi ya dabaibaye wasu jihohi saboda fargabar zuwan ƙarshen wa'adin amfani da tsofaffin kuɗin, wani babban jami'in CBN, ya gaya wa Daily Trust yadda za a janye tsofaffin kuɗin.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda sun tare babbar hanya a Zamfara, sun halaka mutane da dama tare da sace wasu masu yawa

Ya tabbatarwa da ƴan Najeriya cewa ka da su yi fargaba dangane da wa'adin ranar 31 ga watan Disamba, inda ya ƙara da cewa babban bankin a hankali zai janye tsofaffin kuɗin domin kada a wahalar da jama'a.

A kalamansa:

"Dukkaninsu halastattun kuɗi ne. Ƴan Najeriya su cigaba da amfani da su. Babu buƙatar jin fargaba dangane da wa'adin."
"Ba za mu bari ƴan Najeriya su sake shiga cikin wahalar da suka shiga a farkon shekarar nan ba. A hankali za a janye tsofaffin takardun kuɗin. Ba za a yi gaggawa ba."

Malami Ya Ce Ya Kamata a Daina Amfani da Sabbin Kudi

A wani labarin kuma, fasto Babatunde Elijah Ayodele, ya buƙaci CBN da ya sanya a daina amfani da sabbin takardun kuɗin da tsohon shugaban ƙasa Buhari ya kawo.

Babban faston ya bayyana cewa babu alheri a tattare da kuɗaɗen, kuma an yi su da mugun nufin dagula tattalin arziƙin Najeriya ne.

Asali: Legit.ng

Online view pixel