Majalisar Wakilai Ta Ba AGF Wa'adin Sa'o'i 72 Domin Bayar da Ba'asi Kan N100bn Na Tallafin COVID-19

Majalisar Wakilai Ta Ba AGF Wa'adin Sa'o'i 72 Domin Bayar da Ba'asi Kan N100bn Na Tallafin COVID-19

  • Majalisar wakilai ta bai wa AGF, Oluwatoyin Madein wa'adin sa'o'i 72 domin ta bayar bayani kan naira biliyan 100 na tallafin COVID-19
  • Kwamitin majalisar mai kula da asusun gwamnati ya zargi AGF da ƙin biyayya ga matsayar kwamitin na ta miƙa rahoto kan kuɗaɗen a ranar 27 ga watan Oktoba
  • Rahoton zai yi bayani kan yadda aka kashe kuɗaɗen tallafin korona musamman a cikin shekarar 2020 har zuwa 2022

Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum da nishaɗi

FCT, Abuja - An bai wa Akanta Janar ta tarayya, Oluwatoyin Madein, wa'adin sa'o'i 72 domin gabatar da cikakken rahoto kan yadda aka yi amfani da kuɗaɗen tallafin COVID-19 har Naira biliyan 100.

Gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ce ta saki kuɗaɗen ga ma'aikatu da hukumomi (MDA) a tsakanin shekarar 2020 zuwa 2022.

Kara karanta wannan

Hajjin 2024: An bayyana kudin da maniyyata ka iya biya domin zuwa Saudiyya

An ba AGF wa'adi kan kudaden tallafin COVID-19
Majalisar wakilai ta bukaci AGF ta mika mata rahoto kan yadda aka kashe kudaden tallafin COVID-19 Hoto: House of Reps/@Imranmuhdz
Asali: UGC

Kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito, shugaban kwamitin majalisar a kan asusun gwamnati, Hon. Bamidele Salam (PDP-Osun) ya bayyana cewa majalisar wakilai ta umarci kwamitin ya binciki yadda aka kashe kuɗaɗen tallafin COVID-19 musamman daga 2020 zuwa 2022.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hon. Salam ya ce bayar da wa'adin ya biyo bayan gazawar AGF wajen yin biyayya da matsayar da kwamitin ya cimmawa na ta miƙa masa rahoton a ranar 27, ga watan Oktoba, rahoton Daily Trust ya tabbatar.

AGF ba ta kawo rahoto a ranar da aka ce mata ba

Ɗan majalisar ya bayyana cewa kwamitin ya sanar da ita cewa, idan akwai wani dalili da zai sanya ba za ta iya gabatar da rahoton a ranar 27 ga watan Oktoba ba, ta sanar domin a ƙara mata lokaci.

Saboda wuce lokacin ba tare da miƙa rahoton ba, sai kwamitin ya umarci AGF da ta miƙa rahoton kafin zuwa lokacin tashi aiki a ranar Juma'a, 3 ga watan Nuwamban 2023.

Kara karanta wannan

Babban Bankin Najeriya CBN ya bayyana lokacin da za a daina amfani da tsofaffin takardun kudi

Majalisar dai ta cimma matsayar binciken yadda aka kashe kuɗaden ne bayan amincewa da wani kuɗiri wanda ya yi zargin an karkatar da N100bn na tallafin COVID-19 daga shekarar 2020 zuwa 2022.

An Kawo Karshen COVID-19

A baya rahoto ya zo cewa hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta bayyana cewa an kawo ƙarshen annobar cutar COVID-19 da ta karya tattalin arziƙin duniya.

Hukumar ta bayyana hakan ne bayan shekara uku da ɓarkewar cutar wacce ta yi sanadiyyar rasuwar mutane masu yawa a faɗin duniya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel