Wike Ya Sha Alwashin Daukar Tsattsauran Mataki Kan Wasu Gine-Gine a Abuja, Ya Fadi Dalili

Wike Ya Sha Alwashin Daukar Tsattsauran Mataki Kan Wasu Gine-Gine a Abuja, Ya Fadi Dalili

  • Nyesom Wike, ministan babban birnin tarayya ya ce gwamnatinsa za ta kwace gine-ginen da aka yi watsi da su ba tare da an kammala ba a Abuja
  • Wike ya bayyana cewa gine-ginen da ba a kammala ba a Abuja sun zama mabuyar masu laifi kuma cewa gwamnati za ta karbe su
  • Ministan ya nuna yakinin cewa tsaro zai inganta a Abuja da zaran motocin bas na zamani sun fara aiki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullunm

FCT, Abuja - Nyesom Wike, ministan babban birnin tarayya ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta rushe gine-ginen da aka yi watsi da su a Abuja, yana mai cewa wadannan gine-gine sune mabuyar masu laifi a yanzu.

Kara karanta wannan

Wike ya lissafa manyan zunubai 3 da Gwamna Fubara ya aikata da yasa yake so a tsige shi

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto, ministan ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, 1 ga watan Nuwamba, yayin da ya gurfana a gaban kwamitin majalisar dattawa don kare naira miliyan 100 da aka warewa Abuja cikin karin kasafin kudin 2023.

Wike ya sha alwashin ruguza gine-gine a Abuja
Abuja: Wike Ya Gurfana a Gaban Majalisa, Ya Bayyana Gine-Ginen Da Zai Rushe, Ya Fadi Dalili Hoto: Nyesom Wike
Asali: Twitter

Wike ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Za mu rushe dukkanin gine-ginen da aka yi watsi da su a Birnin tarayya. Za kuma mu kwace duk wadannan gine-gine saboda mun gano cewa sune mabuyar miyagu."

Wike ya bayyana yadda za a kawo karshen rashin tsaro a Abuja

Ministan ya kuma nuna yakinin cewa abubuwa za su daidaita a Abuja ta fuskacin tsaro, yana mai cewa gine-ginen da aka yi watsi da su sun zama manyan mabuyar masu laifi.

Ya kara da cewar batun masu satar mutane a motar haya zai sama tarihi a Abuja da zaran motocin bas sun fara aiki kuma cewa rashin tsaro a babban birnin tarayyar Najeriya zai inganta a kullum, rahoton The Eagles.

Kara karanta wannan

Wike ya karyata rade-radi, ya shaidawa Gwamnoni silar rigimarsa da Gwamnan Ribas

Wike ya gargadi manya a Abuja

A wani labarin, ministan Abuja, Nyesom Wike, ya ja-kunnen wadanda basa biyan kudin harajin filayensu.

Wike ya nemi duk wadanda ake bi bashi da su sauke nauyin da yake kan su kafin wa’adin da ya diba ya cika.

Ministan ya ce idan har lokacin afuwar da ya diba ya wuce, toh za a ga aiki da cikawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel