"Ba Matsala Ne Ba Idan An Samu Rashin Jituwa Tsakanin Da da Mahaifi", Gwamna Fubara

"Ba Matsala Ne Ba Idan An Samu Rashin Jituwa Tsakanin Da da Mahaifi", Gwamna Fubara

  • A karon farko gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara ya yi magana kan rashin jituwarsa da magabacinsa Nyesom Wike
  • Gwamna Fubara ya bayyana cewa ba wani abu ba ne domin sun samu saɓani a tsakaninsa da ministan na birnin tarayya Abuja
  • Gwamnan ya yi nuni da cewa za su warware duk wani rashin jituwa da ke tsakaninsu domin ɗa da mahaifi ma akan saɓa

Wakilin Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar fiye da shekara biyar wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum da nishaɗi

Jihar Rivers - Gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara, a ranar Laraba, ya bayyana ƙwarin gwiwarsa kan warware rikicin siyasar da ke tsakaninsa da magabacinsa, Nyesom Wike.

Gwamna Fubara ya ce babu laifi uba da ɗansa su samu matsala, yana mai jaddada cewa, idan akwai matsala za a warware ta, cewar rahoton Channels tv.

Kara karanta wannan

"Mun shirya": Rabiu ya gaya wa Tinubu sabon farashin siminti, yayin da yan kasuwa ke siyarwa a N5000

Gwamna Fubara ya yi magana kan rikicinsa da Wike
Gwamna Fubara ya yi nuni da cewa za su sabanin da ke tsakaninsu shi da Wike Hoto: Sir Siminalayi Fubara
Asali: Facebook

Gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin da babban hafsan hafsan sojojin Najeriya, Janar Christopher Musa ya jagoranci tawagar sojoji zuwa gidan gwamnati da ke Port Harcourt, babban birnin jihar Rivers.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Fubara ya sake jaddada kuɗirin Shugaba Bola Tinubu na samar da zaman lafiya da tsaro a kasar nan, musamman a lokacin zaɓukan gwamnoni da ke tafe.

A kalamansa:

"Ga jiharmu mai daraja, na san kowa yana mamakin abin da ke faruwa, abin da ba ya faruwa. Muna lafiya, babu wata matsala."
"Idan muna da matsala ta cikin gida, za a warware ta sannan komai zai koma daidai."
"Babu laifi idan uba da ɗansa sun samu saɓani, idan akwai wata matsala, amma bana tsammanin akwai wani abu, ko menene, tabbas za mu warware matsalar."

Gwamonin PDP sun gana kan Wike, Fubara

Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya karɓi baƙuncin takwarorinsa gwamnonin jam'iyyar PDP domin tattauna batun tsige Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Rivers.

Kara karanta wannan

Gwamnonin PDP za su gana da Ministan Tinubu kan muhimmin batu 1, bayanai sun fito

Taron wanda ya samu halartar manyan jiga-jigan jam'iyyar PDP zai yi duba kan takun saƙan da ake yi a tsakanin ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, da magajinsa Gwamna Siminalayi Fubara.

Tinubu Ya Shiga Tsakani a Rikicin Wike, Fubara

A wani labarin kuma, shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya shiga tsakani a rikicin siyasar da ya taso a tsakanin Gwamna Fubara da Nyesom Wike.

Shugaban ƙasar ya buƙaci manyan ƴan siyasar biyu na jihar Rivers da su zauna lafiya a tsakaninsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel