Manyan Labarai A Yau
Wasu ƴan ta'adda mayaƙan ƙungiyar Boko Haram sun salwantar da rayukan mutim 16 a wani ƙazamin hari da suka kai ƙaramar hukumar Geidam ta jihar Yobe.
Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya karɓi baƙuncin takwarorinsa na PDP kan batun tsige gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara, mai takun saƙa da Wike.
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya gana da gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, kan batun tsige Fubara.
Kotun ƙoli ta ɗage sauraron ƙarar da jam'iyyar APGA ta shigar domin neman a tsige gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma, na jam'iyyar APC mai mulki a jihar.
Kotun ɗaukara ƙara ta zartar da hukunci kan soke takarar ɗan takarar gwamnan APC na jihar Bayelsa. Kotun ta warware hukuncin soke takarar Timipre Sylva.
Gwamnatin jihar Rivers ta musanta rahotannin cewa Gwamna Siminalayi Fubara ya kori shugaban ma'aikatansa da bayar da umarnin korar shugabannin kananan hukumomi.
An gano rikicin siyasar jihar Ribas yana da nasaba da matakin da Gwamna Siminalayi Fubara ya dauka na farfado da manufar Rotimi Amarchi, wannan ya fusata Wike.
Wata matar aure ta haifi tagwaye kasa da awanni 24 bayan mijinta ya mutu. Bidiyon matar da yaran nata ya tsuma zukatan mutane da dama a soshiyal midiya.
Kotun daukaka kara reshen Abuja ta tabbatar da Natasha Akpoti-Uduagan a matsayin sahihiyar yar takarar da ta lashe zaben sanata mai wakiltar Kogi ta tsakiya.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari