Manyan Labarai A Yau
Limamin katolika na Sokoto, Bishop Matthew Kukah, ya bayyana cewa mutanen da ke da alhakin haifar da matsalolin Najeriya suma basu tsira ba kamar kowa.
Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Rivers da ubangidansa a siyasance Nyesom Wike na ta takun saƙa. An jeranto sauran gwamnonin da ke da iyayen gida a siyasance.
Rikicin shugabancin da ke tsakanin Sarkin Sasa, Alhaji Haruna Maiyasin da Sarkin Hausawa na Ibadan, Alhaji Ali Zungeru na kawo tashin hankali a al'ummar Hausawa.
Shugaban kasa Tinubu, Sultan na Sakkwato, Sa’ad Abubakar da wasu Musulman yan Najeriya 13 da suka shiga jerin musulman duniya 500 masu fada a ji a 2024.
Tsohon gwamnan jihar Cross Rivers, Ben Ayade, ya yi rashin nasara a kotun ɗaukaka ƙara. Kotun ɗaukaka ƙarar ta yi fatali da ƙarar da ya ɗaukaka kan zaɓen Sanata.
Tsohon babban hafsan sojin ƙasa, Tukur Buratai ya bayyana waɗanda suka haifar da matsalar rashin tsaro a Najeriya, inda ya ɗora laifin kan ƴan siyasa.
Kotun ɗaukaka ƙara ta sanya ranar da za ta fara sauraron ƙarar da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya shigar kan nasarar Nasiru Yusuf Gawuna a kotun zaɓe.
Gwamnatin Amurka ta gargadi yan kasarta da ke Najeriya, inda ta sanar da su kan "gagarumin barazana" na tsaro kan fitattun otel a manyan biranen kasar.
Shehu Sani ya yi tsokaci kan rikicin siyasar da ke aukuwa a jihar Rivers, inda ya ba Gwamna Siminalayi Fubara, shawara kan yadda zai magance Wike.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari