'Yan Bindiga Sun Kai Kazamin Hari a Jihar Zamfara, Sun Yi Awon Gaba da Mutum 5

'Yan Bindiga Sun Kai Kazamin Hari a Jihar Zamfara, Sun Yi Awon Gaba da Mutum 5

  • Ƴan bindiga sun kai sabon hari a garin Maru inda suka halaka mutum ɗaya tare da yin awon gaba da wasu mutum biyar
  • Miyagun ƴan bindigan a yayin harin da suka kai sun kuma ƙona wata motar sintiri ta ƴan sanda ƙurmus
  • Mazauna garin Maru sun koka kan yadda ƴan bindiga ke addabarsu da hare-hare ba ƙaƙƙautawa a garin

Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum da nishaɗi

Jihar Zamfara - Wasu ƴan bindiga ɗauke da makamai sun kai hari a garin Maru hedikwatar ƙaramar hukumar Maru a jihar Zamfara.

Ƴan bindigan a yayin harin sun kashe mutum ɗaya, sannan suka ƙona wata motar ƴan sanda da ke sintiri a kan titi, sannan suka yi awon gaba da mutum biyar ciki har da wani malami na Kwalejin Ilimi (COE) ta Maru.

Kara karanta wannan

Tukur Buratai ya fasa kwai kan ainihin wadanda suka kawo rashin tsaro a Najeriya

'Yan bindiga sun sace mutum biyar a Zamfara
'Yan bindiga sun halaka mutum daya da sace mutum biyar a Zamfara Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Rahotanni sun nuna cewa ƴan bindigar wadanda suka zo da yawa sun afkawa garin Maru da safiyar Lahadi, 5 ga watan Nuwamba da nufin yin awon gaba da mazauna garin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda harin ya auku

Wani mazaunin garin Malam Yusuf Musa ya shaida wa jaridar Nigerian Tribune cewa ƴan bindigar sun isa garin Maru ɗauke da manyan makamai.

"Lokacin da suka shiga garin, sai suka fara harbi lokaci-lokaci domin tsoratar da mutane." A cewarsa.

Bugu da ƙari, Mallam Mohammed Amadu, ɗan asalin garin, ya bayyana cewa:

"Ƴan bindigan waɗanda suka zo da yawa, sun dira garin cikin dare inda suka farmaki al'umma. Da yawa daga cikinmu mun gudu zuwa cikin daji domin tsira daga harin."
"An sace mata uku da maza biyu da suka haɗa da Lawali Dan Muazu da Nasiru Anka malami a Kwalejin Ilimi ta Maru."

Kara karanta wannan

Wasu matasa 2 sun jefa kansu a babbar matsala kan motar simintin Ɗangote

Ƴan bindiga na yawan kai hari a Maru

Ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici, inda yace mutanen garin Maru na fuskantar hare-hare ba kakkautawa daga ƴan bindiga. A cewarsa harin na yau shi ne karo na uku cikin kwanaki 11.

Ya koka da cewa ƴan bindigan sun kuma halaka wani mai gyaran waya mai suna Abdul, wanda ke da shago a babbar kofar shiga tashar motan Maru

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ba a samu jin ta bakin mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar Zamfara, ASP Yazid Abubakar ba, saboda kiran da aka yi masa ta wayarsa da dama bai amsa ba, kuma an kashe layukan wayarsa.

An Halaka Mutane a Babbar Hanya

A wani labarin kuma, ƴan ta'adda sun tare babbar hanyar Funtua-Gusau a jihar Zamfara inda suka halaka mutanen da ba a san adadin su ba.

Miyagun ƴan ta'addan waɗanda suka tare motocin a kusa da garin Tsafe, sun kuma yi awon gaba da wasu mutanen masu yawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel