Abba vs Gawuna: Kotun Daukaka Kara Ta Sanya Ranar Fara Sauraron Shari'ar Gwamnan Kano

Abba vs Gawuna: Kotun Daukaka Kara Ta Sanya Ranar Fara Sauraron Shari'ar Gwamnan Kano

  • Kotun ɗaukaka ƙara ta sanya ranar fara sauraron ɗaukaka ƙarar da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi kan zaɓen gwamnan Kano
  • Kotun ta sanya a ranar Litinin, 6 ga watan Nuwamba a matsayin ranar da za ta fara sauraron ƙarar da Gwamna Abba ya ɗaukaka
  • Gwamna Abba ya ɗaukaka ƙara ne bayan kotun zaɓe ta tsige shi daga muƙamin gwamnan Kano tare da bayyana Gawuna a matsayin wanda ya lashe zaɓe

Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum da nishaɗi

FCT, Abuja - Kotun daukaka ƙara da ke zamanta a birnin tarayya Abuja ta sanya ranar Litinin, 6 ga watan Nuwamba domin sauraron ƙarar da Gwamna Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) ya ɗaukaka.

Gwamna Abba Kabir ya ɗaukaka ƙara kan abokin takararsa na jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Nasiru Yusuf Gawuna, bayan kotun zaɓe ta bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar Kano, cewar rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Kotun daukaka kara ta yi hukunci kan kujerar dan majalisar APC a jihar Edo

Kotun daukaka kara ta sanya ranar fara sauraron karar Gwamna Abba
Kotun daukaka za ta fara sauraron karar Abba Yusuf a ranar Litinin Hoto: Abba Kabir Yusuf, Nasir Yusuf Gawuna
Asali: Facebook

Gwamnan ya shigar da ƙarar ne domin ƙalubalantar soke zaɓensa da kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan jihar Kano ta yi, rahoton Vanguard ya tabbatar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda Abba ya yi rashin nasara a Kotu

Kotun mai alƙalai uku ƙarƙashin jagorancin mai shari'a Oluyemi Akintan Osadebay ta tsige Yusuf a ranar 20 ga Satumban 2023, ta hanyar bayyana ƙuri’unsa 165,663 a matsayin marasa inganci saboda "ba INEC ta sanya hannu ko ta buga musu tambari ba."

Ɓangarorin da ke cikin ƙarar sun haɗa da Gwamna Yusuf da jam'iyyarsa, NNPP da jam'iyyar adawa ta APC da kuma hukumar zabe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC).

INEC ta bayyana Gwamna Yusuf a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan na ranar 18 ga watan Maris, 2023 bayan ya samu ƙuri'u 1,019,602 yayin da Gawuna ya samu ƙuri'u 890,705.

Kara karanta wannan

Tsohon gwamnan APC ya yi rashin nasara bayan kotu ta yanke hukunci kan zaben sanata

Sai dai, da kotun ta cire ƙuri’u 165,663 daga ƙuri’un Gwamna Yusuf inda ƙuri'unsa suka koma 853,939, ƙasa da 30,000 na ƙuri'u 890,705 da Gawuna ya samu.

Sakamakon haka, kotun ta bayyana ɗan takarar jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamna tare da umartar hukumar zabe ta INEC da ta janye takardar shaidar cin zaɓen Gwamna Yusuf.

Legit Hausa ta samu jin ta bakin wani mai goyon bayan jam'iyyar NNPP baya mai suna Ibrahim Zulkiful, wanda ya nuna ƙwarin gwiwarsa cewa za su samu nasara a kotu.

Ibrahim ya nuna cewa suna da ƙwarin gwiwar yin nasara a kotun domin kotun zaɓe ta yi kuskure a hukuncin da ta yanke.

Ya bayyana cewa tabbas kotun za ta yi adalci wajen soke hukuncin da kotun zaɓen ta yi, saboda a cewarsa kotun zaɓen ba ta da hurumin soke ƙuri'un da Gwamna Abba ya samu.

Wadanda Suka Yi Nasara a Kan Gwamna Abba a Kotu

Kara karanta wannan

APC da LP sun gamu da cikas, Kotun ɗaukaka ƙara ta yanke hukunci kan nasarar 'yan majalisar tarayya 2

A wani labarin kuma, mun kawo muku jerin waɗanda suka yi nasara kan gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, a kotu.

Gwamnan ya yi rashin nasara kan shari'ar zaɓen gwamnan Kano, sannan ya yi rashin nasara a ƙarar da ƴan kasuwa suka maka shi bayan ya ruguje musu shaguna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel