Arewa Ba Ta da Ikon Yin Korafi Kan Nade-Naden Shugaba Tinubu, Kungiyar Arewa
- Ƴan Arewa da dama sun yi ƙorafi kan yadda Shugaba Tinubu yake fifita yankin Kudu maso Yamma wajen yin yin rabon muƙamai a gwamnatinsa
- Sai dai, ƙungiyar NYLF ta yi nuni da cewa ƴan Arewa ba su da ikon yin ƙorafi kan yadda shugaban ƙasar yake raba muƙamansa
- Shugaban ƙungiyar na ƙasa ya yi nuni da cewa a lokacin mulkin Buhari haka ya riƙa fifita yankin Arewa wajen ba da muƙamai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum da nishaɗi
Jihar Ogun - Ƙungiyar Shugabannin Matasan Arewa (NYLF) ta ce ƴan Arewa ba su da hurumin kokawa kan naɗe-naɗen da Shugaba Bola Tinubu ya ke yi, cewar rahoton Daily Trust.
Wasu shugabannin yankin sun zargi Tinubu da karkatar da muƙamai masu gwaɓi zuwa yankin Kudu maso Yamma, yankin da (Tinubu) ya fito.
Wani Malamin addinin Islama, Ahmad Gumi, a wani wa'azin da ya gabatar a baya-bayan nan, ya caccaki Tinubu kan naɗa Kiristocin Kudu a wasu muhimman muƙamai, inda ya ce shugaban ƙasar ba zai sake samun wa'adi na biyu ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Malamin ya kuma zargi shugaban ƙasar da yin amfani da yankin Arewa wajen zuwa fadar shugaban ƙasa kawai domin cimma wata manufa ta nufin rage tasirin siyasar yankin.
Bai kamata ƴan Arewa su yi ƙorafi ba, cewar NYLF
Da yake jawabi ga manema labarai a Abeokuta, jihar Ogun, shugaban NYLF na ƙasa, Elliot Afiyo, ya ce Tinubu na ƙara fifita ba wani yanki muƙamai wanda ya gaji hakan a wajen magabacinsa, Muhammadu Buhari.
Ya kara da cewa Buhari ya samar da giɓin 80:20 ga Arewa da Kudu wajen bayar da muƙamai a gwamnatinsa, rahoton shafin Osundefender ya tabbatar.
Elliot, ya roki Tinubu da ya cike wawukeken giɓin domin ƙasar nan ba za ta cigaba da tafiya a kan ‘kuskure’ ba.
A kalamansa:
Zan iya cewa ƴn Arewa ba su da ƴancin yin korafin cewa an fi fifita wani yanki a naɗe-naɗen. Ba mu da haƙƙin yin ƙorafi."
"Amma a matsayina na ɗan ƙasa, zan yi tambaya, shin za mu iya cigaba a haka? Idan muka samu shugaban ƙasa ɗan Igbo zai naɗa Igbo. Ina za mu je a matsayin ƙasa? Domin haka akwai buƙatar mu daidaita shi."
An Maka Tinubu Kara a Kotu
A wani labarin kuma, ƙungiyar SERAP ta maka Shugaba Tinubu ƙara a gaban kotu kan ɓacewar kuɗaɗen shiga na man fetur da kuɗaden gyaran matatun man fetur.
Ƙungiyar dai ta shigar da ƙarar ne bisa zargin ɓacewar $15bn kuɗaɗen shiga na man fetur da N200bn kuɗaɗen gyaran matatun man fetur.
Asali: Legit.ng