Tukur Buratai Ya Fasa Kwai Kan Ainihin Wadanda Suka Kawo Rashin Tsaro a Najeriya

Tukur Buratai Ya Fasa Kwai Kan Ainihin Wadanda Suka Kawo Rashin Tsaro a Najeriya

  • Laftanar Janar Tukur Buratai ya yi magana kan rashin tsaron da ya dade yana addabar ƙasar nan
  • Tsohon babban hafsan sojin ƙasan ya bayyana cewa ƴan siyasa ne suka samar da rashin tsaro a ƙasar nan
  • Buratai ya kuma caccaki waɗanda suka riƙa sukarsa kan matsalar tsaro lokacin da yake a bakin aiki

Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum da nishaɗi

Ibadan, jihar Oyo - Tsohon babban hafsan sojin ƙasa (COAS), Laftanar Janar Tukur Buratai, ya ce rashin tsaro da kasar nan ke fama da shi, ƴan siyasa ne suka samar da shi.

Buratai ya bayyana hakan ne a ranar Juma'a, 3 ga watan Nuwamba, yayin wata lakca da aka shirya domin bikin cika shekaru 65 da kafa kungiyar tsofaffin daliban jami'ar Ibadan, cewar rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP da kujerarsa ke tangal-tangal ya nemi afuwar talakawan jiharsa kan abu 1 da ya faru

Buratai ya yi magana kan rashin tsaro
Tukur Buratai ya ce yan siyasa ne suka haifar da rashin tsaro Hoto: Tukur Buratai
Asali: Facebook

Ya kuma yi kakkausar suka ga masu sukar sa da ke kira da a kore shi saboda rashin tsaro a ƙasar a lokacin da yake kan mulki, yana mai cewa irin wannan kiran ya samo asali ne daga son zuciya maimakon tantance haƙiƙanin aikinsa, rahoton Guarɗian ya tabbatar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Buratai ya magantu kan matsalar rashin tsaro

A kalamansa:

"Waɗannan mutanen ta yiwu suna da wani ra'ayi mara kyau kan Buratai bisa wasu dalilai da suka haɗa da son zuciya ko son rai waɗanda ba su da alaƙa da abin da zai iya yi."
"Yana da kyau a fuskanci rin waɗannan batutuwan kan tsaron ƙasa da zuciya ɗaya, mayar da hankali kan abubuwan da ke da muhimmanci maimakon son zuciya da rashin fahimta."
"Majalisar tarayya sau biyu tana amincewa da ƙudirin neman korar hafsoshin tsaro. Shugaban ƙasa Buhari ya gaya wa majalisar tarayya ta tara da ta mayar da hankali kan aikin da ke gabanta. Idan an fassara abun da kyau, kiran da majalisar ta yi na ɓata dimokuraɗiyya da sojoji ne."

Kara karanta wannan

Mutum 11 sun rasu wasu 11 sun samu raunika a wani kazamin hatsarin mota a jihar Kebbi

"Wannan ya kamata ya zama darasi ga ƴan siyasa. Rigima ce kai tsaye zargin hafsoshin tsaro kamar su ne suka fara rashin tsaro. Matsalar rashin tsaro da ake fuskanta a ƙasar nan tun shekarar 2009 ƴan siyasa ne suka kirkiro ta. Indai da gaske a ke, za a iya kawo ƙarshen matsalar."

Ya shawarci ƴan siyasa da ma'aikatan gwamnati da su cigaba da rayuwa ta hanyar gujewa cin hanci da rashawa wanda a cewarsa, ya dabaibaye harkar siyasar kasar nan tsawon shekaru da dama, tare da zubar da mutuncin jama'a da hana samun cigaba.

An Nada Buratai Sarauta

A wani labarin kuma, Sarkin Biu ya naɗa tsohon babban hafsan sojin ƙasa, Laftanar Janar Tukur Buratai, sarauta a masauratar Biu.

Mai martaba Dr Umar Mustapha na II ya naɗa Buratai sarautar Betaran Biu, a ranar 27 ga watan Oktoban 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel