Kotun Daukaka Kara Ta Yi Hukunci Kan Kujerar Dan Majalisar APC a Jihar Edo

Kotun Daukaka Kara Ta Yi Hukunci Kan Kujerar Dan Majalisar APC a Jihar Edo

  • Kotun ɗaukaka ƙara ta zartar da hukunci kan shari'ar da ake kan kujerar ɗan majalisar wakilai ta mazabar Ovia a jihar Edo
  • Kotun ta tabbatar da nasarar Dennis Idahosa na jam'iyyar APC ya matsayin sahihin wanda ya lashe zaɓen
  • Ƙararrakin ɗa ƴan takarar jam'iyyun PDP da LP suka shigar a gaban kotun ba du yi nasara ba inda kotun ta yi fatali da su

Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum da nishaɗi

Jihar Edo - Kotun ɗaukaka ƙara ta tabbatar da sake zaɓen Mista Dennis Idahosa na jam'iyyar All Progressives Congress (APC), a matsayin zaɓaɓɓen ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazaɓar tarayya ta Ovia a jihar Edo, cewar rahoton Tribune.

Kotun ɗaukaka ƙara ta amince da kotun sauraron ƙararrakin zaɓen ƴan majalisu, wacce tun farko ta yi watsi da ƙararrakin da Omosede Igbinedion na PDP, da Misis Epelle Osayuki ta Labour Party (LP), suka shigar da ke ƙalubalantar nasarar Idahosa a zaɓen na ranar 25 ga watan Fabrairun 2023.

Kara karanta wannan

Abba vs Gawuna: Kotun daukaka kara ta sanya ranar fara sauraron shari'ar gwamnan Kano

Dennis Idahosa ya yi nasara a kotu
Kotun daukaka kara ta tabbatar da nasarar Dennis Idahosa Hoto: Hon. Dennis Idahosa
Asali: Facebook

Da yake mayar da martani kan hukuncin da aka yanke ranar Asabar, Idahosa ya ce sakamakon hukuncin da aka yanke, an tabbatar da cewa al’ummar mazabar tarayya ta Ovia ba za su sake barin wani, ya zo ya yi musu katsalandan ba, ba tare da sahalewarsu ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Mista Friday Aghedo, ya fitar, ɗan majalisar ya bayyana cewa bai taɓa damuwa kan ƙarar ba, saboda ya san cewa shi al'ummar mazaɓar suka zaɓa, rahoton Igbere tv ya tabbatar.

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

"Jama’a sun ga bambani a mazaɓar tarayya a cikin shekaru huɗu da suka gabata, kuma ni Idahosa na yi rantsuwar tabbatar da wannan nasara wacce za ta ba ni damar cigaba da yi wa jama'a hidima."

Kara karanta wannan

APC da LP sun gamu da cikas, Kotun ɗaukaka ƙara ta yanke hukunci kan nasarar 'yan majalisar tarayya 2

"Wannan nasarar ba ni kaɗai zan yi murnar samun ta ba. Waɗanda suka fi cin gajiyar wannan nasarar su ne al'ummar mazaɓar tarayya ta Ovia."

Kotu Ta Tabbatar da Nasarar Sanatan APC

A wani labarin kuma, kotun ɗaukaka ƙara ta tabbatar da nasarar Sanata Ifeanyi Uba a matsayin sanatan Anambra ta Kudu.

Kotun ta yi watsi da ƙararrakin da ƴan takarar jam'iyyun APGA, PDP da LP suka shigar saboda rashin ingancinsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel