Wike vs Fubara: Cikakken Jerin Gwamnonin Najeriya Da Ke da Shahararrun Iyayen Gida a Siyasa

Wike vs Fubara: Cikakken Jerin Gwamnonin Najeriya Da Ke da Shahararrun Iyayen Gida a Siyasa

Rikicin siyasar da ya dabaibaye jihar Ribas dai an bayyana shi a matsayin rigimar da aka saba yi tsakanin ubangida da yaronsa, inda da dama daga cikin masu sharhi suka nuna yatsa ga tsohon gwamnan jihar, Nyesom Wike, wanda yanzu shi ne ministan babban birnin tarayya (FCT).

Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum da nishaɗi

Gwamna Siminalayi, a yunƙurinsa na sasantawa da ubangidansa, Wike, an ga yadda ya nemi afuwar jama'a game da rikicin baya-bayan nan da ya faru a jihar tare da ƙoƙarin nesanta kansa da majalisar dokokin jihar tare da yabawa sanya bakin Shugaba Bola Tinubu.

Gwamnonin da ke da iyayen gida a siyasa
Gwamnonin Najeriya da ke da iyayen gida na siyasa Hoto: Uba Sani, Babajide Sanwo-Olu, Abba Kabir Yusuf
Asali: Twitter

A nasa ɓangaren, Wike ya tsaya tsayin daka wajen kare tsarin siyasar da ya bari a jihar, inda ya ƙara da cewa ba zai bari wani ya zo kusa da ita ba, yayin da ya koka kan yadda Fubara ya bi sahun maƙiyansa na siyasa da suka yaƙe shi lokacin yaƙin neman zaɓen (Fubara).

Kara karanta wannan

Ministan Tinubu da hatsarin jirgin sama ya rutsa da shi ya magantu, ya faɗi halin da yake ciki

Hakazalika Wike yana samun goyon bayan dattawan jihar, waɗanda suka tunatar da Fubara yadda magabacinsa ya mara masa baya da shi da sauran masu riƙe da muƙaman siyasa a jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai, yana da kyau a lura cewa ba Fubara ba ne kawai gwamna mai ci a Najeriya wanda ya samu wannan muƙamin ta hanyar taimakon Ubangida ba.

Ga jerin gwamnonin Najeriya wadanda iyayen gidansu suka shahara:

Abba Kabir Yusuf

Gwamnan jihar Kano wanda aka fi sani da Abba Gida Gida, sanannen ɗan Kwankwasiyya ne kuma surukin tsohon gwamnan jihar, Rabiu Kwankwaso.

Masana harkokin siyasa da dama na sane da cewa Kwankwaso ubangidan siyasa ne ga gwamnan jihar Kano, wanda ya karɓi mulki a hannun tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje.

Babajide Sanwo-Olu

Jihar Legas dai jiha ce ta gwagwarmayar mulki, samun saɓani da sulhu a ƙarƙashin jagorancin ubangida a siyasar jihar, Shugaba Bola Tinubu, tun dawowar mulkin dimokuradiyya a 1999, lokacin da Tinubu ya zama gwamnan jihar.

Kara karanta wannan

Shehu Sani ya shawarci Gwamna Fubara kan yadda zai yi maganin Wike

Shugaba Tinubu dai ya shahara kuma kowa ya san shi a matsayin ubangida a siyasar Legas, nuna goyon bayansa ga duk wani ɗan takara a jihar yana da matukar muhimmanci a harkokin siyasar jihar.

Uba Sani

Ba za a iya bayyana ɓullowar Uba Sani da shaharar da ya yi a siyasar Kaduna ba, ba tare da an ƙi ambatar tasirin tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufai.

El-Rufai ya yi tasiri sosai a siyasar Arewa, inda aka ruwaito mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya taka rawar gani wajen ƙin amincewa da shi a matsayin minista a gwamnatin Shugaba Tinubu da majalisar dattawa ta yi.

Dikko Umar Radda

Gwamna Dikko Radda na jihar Katsina ya samu nasarar lashe zaɓen gwamnan jihar Katsina a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar APC.

Sai dai, ba zai yiwu a yi batun nasararsa ba, ba tare da bayyana rawar da tsohon gwamnan jihar Aminu Bello Masari ya taka ba.

Kara karanta wannan

Tukur Buratai ya fasa kwai kan ainihin wadanda suka kawo rashin tsaro a Najeriya

Masari tun a lokacin zaɓen fidda gwani ya nuna Dikko ne ɗan takararsa sannan ya yi babbar huɓɓasa wajen ganin ya ɗare kan mulkin jihar.

Ahmed Aliyu

A siyasance Gwamna Ahmed Aliyu na jihar Sokoto, Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko ne ubangidansa.

Wamakko wanda tsohon gwamnan jihar ne, ya taka muhimmiyar rawa wajen zaman Ahmed Aliyu, gwamnan jihar Sokoto.

Umara Zulum

Mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima ya taka muhimmiyar rawa wajen ganin Farfesa Babagana Umara Zulum ya zama gwamnan jihar Borno.

Shettima ya zaɓo Zulum ya zama gwamnan jihar ne bayan ya gamsu da kamun ludayinsa kan yadda yake da kishin al'umma da mutunta aikinsa.

Gwamnonin da Suka Yaki Iyayen Gidansu

A wani labarin kuma, mun kawo muku jerin gwamnonin da suka yi faɗa da iyayen gidansu a siyasance kuma suka samu nasara.

Daga cikinsu akwai tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya yi takun saƙa da Rabiu Musa Kwankwaso, madugun Kwankwasiyya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel