"Idan Ba'a Kira Ni Dan Midiya Ba Ɗan Uwarki Za'a Kira Ni" Na Hannun Daman Ganduje Ya Wanke Budurwa

"Idan Ba'a Kira Ni Dan Midiya Ba Ɗan Uwarki Za'a Kira Ni" Na Hannun Daman Ganduje Ya Wanke Budurwa

  • DDan takarar gwamnan Kano a zaben 2023 a jam'iyyar PRP, Salihu Tanko Yakasai ya mayar da zazzafan martani ga wata budurwa da ta yi masa ba'a
  • Matashiyar ta yi masa dariya cewa daga dan takarar gwamna na zama dan midiya a jam'iyyar APC
  • Dawisu ya ce midiya aikinsa ne kuma yana alfahari da hakan, inda ya ce koda masinja Ganduje ya ba shi zai karba

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Dan takarar kujerar gwamnan jihar Kano karkashin inuwar Peoples Redemption Party (PRP) a zaben 2023, Salihu Tanko Yakasai, wanda aka fi sani da Dawisu ya yi wa wata budurwa wankin babban bargo.

Dawisu ya caccaki budurwar da ta kira shi dan midiya
“Idan ba’a kira ni dan midiya ba dan uwarki za’a kira ni” Na hannun daman Ganduje ya wanke budurwa Hoto: @dawisu/@flexiblenancy
Asali: Twitter

"Ka ji kunya, dan takarar gwamna ya koma dan midiya", budurwa ga Dawisu

Kara karanta wannan

NDLEA ta gano katafaren gonar da ake noman wiwi a Sokoto, ta cafke mutum daya

Matashiyar mai suna @flexiblenancy a dandalin X dai ta yi ba'a ga Dawisu kan mukamin da jam'iyyar APC ta ba shi na hadimin labarai. ta rubuta a shafin nata:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Ka ji kunya @dawisu kayi takaran kujeran governor a Kano a jam'iyyan PRP bayan ka kasa kawo mutum 5k a Kano kafara licking ass din APC/ganduje don kasamu shiga, abun dariya a rasa me za a baka sai Dan midiya.
"Dan takaran gwamna ya koma dan midiya, ka ji kunya."

Ga wallafar tata a kasa:

Da yake mayar mata da martani. Yakasai wanda ya kasance na hannun daman Ganduje ya bayyana cewa shi dan midiya ne kuma yana alfahari da haka.

Ya kuma jaddada cewar koda masinja Ganduje ya ba shi zai karba domin shi uba ya dauke shi ba ubangida ba.

Kara karanta wannan

Gwamnan Bauchi Bala Mohammed ya yi ganawar sirri da Wike kan zaben 2027, rahoto

Ya rubuta a shafin nasa:

"Sakarya Shashasha! Wannan kwamiti din chairman din National Publicity Secretary ne na APC na kasa, wanda ke binsa ministan labarai ne, sai shugaban ma'aikata na kasa, sai SSA na shugaban kasa kan midiya, kafin a zo ni, an gaya miki irin kungiyar ku ce ta Kwankwasiyya ta mutum daya tak? Ko Masinja Ganduje ya bani zan karba na yi, uba na dauke shi ba ubangida ba.
"Kuma wai ku a tunanin ku idan kun ce min dan media zagi na kuke yi? toh ina da diploma a mass Comm, ina da advance diploma a mass comm, ina da digiri a mass comm, sannan nayi aikin gidan radio shekara 6, nayi aiki da CNN a matsayin mai kawo rahoto, na yi hadimin labarai na Gwamna shekara 6, shekara goma ni nake bada tallan Ajino da Bagco a radio a matsayin mashawarci na midiya da sauransu, inada mabiya 378k a Facebook, ga ku nan kuma na Twitter. Kafin nayi takara midiya sana'a ta ce, idan baa kira ni dan midiya ba 'dan uwarki za'a kira ni? ‍♂️"

Kara karanta wannan

Sabon rikici ya kunno PDP yayin da Atiku da fitaccen gwamna suke neman iko, karin bayani

Kotu ta yi hukunci a shari'ar Abba da Doguwa

A wani labarin, mun ji cewa a ranar Juma'a, 1 ga watar Disamba ne kotu ta yanke hukunci kan karar da Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya shigar, inda yake zargin Alhassan Doguwa da ta'addanci.

Da yake tabbatar da hakan a shafinsa na X, Doguwa ya bayyana cewa Mai shari'a Donatus Okorowo, ya soke umurnin Gwamna Yusuf na sake bitar shawarar doka daga Atoni Janar na jihar kan zargin kisan da ake masa a lokacin zabe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel