Zanga-Zanga Ta Barke a Babbar Jami'a a Najeriya, Bayanai Sun Fito

Zanga-Zanga Ta Barke a Babbar Jami'a a Najeriya, Bayanai Sun Fito

  • Ɗaliban jami'ar Calabar (UNICAL) masu ɗumbin yawa sun fito domin nuna adawarsu da ƙarin kuɗin makarantan da aka yi
  • Ɗaliban sun gudanar da zanga-zanga kan ƙarin kuɗin makarantan da kaso 100% ida suka fito ɗauke da kwalaye
  • Hami'ar ta Calabai dai ta bayyana cewa ƙarin ya zama wajibi ne saboda yanayin da ake ciki kan tattalin arziƙi a ƙasar nan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Calabar, jihar Cross Rivers - Ɗaliban Jami'ar Calabar (UNICAL) da dama a ranar Litinin, 4 ga watan Disamba, sun gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewa da ƙarin kuɗin makaranta da mahukuntan makarantar suka yi.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, ƙarin kudin da aka yi wa sabbin ɗalibai, ɗaliban dake 200l da 300l da ɗaliban da ke a ajin ƙarshe a kwasa-kwasan da ba na kimiyya ba ya kai N111,000, N91,500, da kuma N114,000.

Kara karanta wannan

An bayyana dalili 1 da ya hana Atiku komawa Dubai da zama

Dalibai sun yi zanga-zanga a UNICAL
Zanga-zanga ta barke a UNICAL kan karin kudin makaranta Hoto: Nsikak Ibatt
Asali: Facebook

A halin da ake ciki, an ƙara kuɗin kwasa-kwasan kimiyya zuwa N155,000, N125,000, da kuma N148,000, tare da ƙarin wasu kuɗaɗe daban na N38,500, N21,500, da N21,500 ga kowane fanni.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

UNICAL ta ƙara kuɗin makaranta da kaso 100%

Wasu daga cikin kwalayen da ɗaliban suka fito zanga-zangar da su anyi rubuce-rubuce daban-daban kamar: “Florence Obia, UNICAL ba jami’a ce mai zaman kanta ba, me nene kuma ƙari ɗan kaɗan, a daina tatse mu"

“UNICAL VC, a daina tilasta wa ƴan mata karuwanci”, "Wannan jami'ar tarayya ce, ba cibiyar kasuwanci ba," da sauransu.

An tattaro cewa, kafin ƙarin kuɗin makarantar, sabbin ɗalibai na biyan N64,050, ɗaliban ajin ƙarshe na biyan N52,050, ɗaliban 200l da 400l na biyan N49,500 wanda ya danganta da sashen da suke karatu.

Dalilin da ya sa muka ƙara kuɗin makaranta - UNICAL

Kara karanta wannan

Yan ta'addan ISWAP sun halaka yan sakai 2 a yayin wani farmaki

A cewar mahukuntan jami'ar ta Najeriya, karin kuɗin makarantar ya biyo bayan yanayin tattalin arziki da ake ciki a yanzu da kuma buƙatar da ake da ita na kiyaye tsarin ingantaccen karatun da jami’ar ta shahara da shi.

Jamo'ar ta UNICAL ta bi sahun jami'o'in Najeriya da dama waɗanda suka ƙara kuɗaɗen da ɗalibai ke biya.

Mai Aiki Famfo Ya Gama Jami'a da 'First Class'

A wani labarin kuma, kun ji cewa wani matashin ɗalibi na jami'ar fasaha ta tarayya da ke Imo (:FUTO) wanda ya sha gwagwarmaya a wajen karatunsa ya kammala da darajar farko.

Ɗaliban mai suna Gabriel Eze wanda mahaifinsa ya rasu yana ƙarami ya yi sana'ar gyaran famfo domin ya kammala karatunsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel