Yan Sanda Za Su Fara Kama Duk Wanda Ba a San Tushen Arzikinsa Ba

Yan Sanda Za Su Fara Kama Duk Wanda Ba a San Tushen Arzikinsa Ba

  • Rundunar yan sanda a jihar Delta ta nuna tsananin damuwa kan yawan aikata laifuka kamar su kashe mutane don kudin asiri, garkuwa da mutane da damfara ta intanet
  • Bright Edafe, kakakin hukumar yan sandan, ya alakanta wannan lamari da arzikin wasu mutane da ba a san tushensa ba
  • Ya kuma jaddada cewar rundunar yan sanda ta umurci jami'anta da su kama duk mutanen da ba za su iya bayani kan tushen arzikinsu ba sannan a hukunta su

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Jihar Delta, Asaba - Rundunar yan sandan jihar Delta ta yi kira ga binciken mutanen da ba za su iya yin bayani mai gamsarwa kan tushen arziki da inda suke samun kudaden shigarsu ba, tana mai cew aya kama a bincike su tare da gurfanar da su a gaban kotu.

Kara karanta wannan

Zargin maita: Yan sanda sun kama mutum 2 kan kashe dan uwansu da yunwa a Nasarawa

Kakakin rundunar, Bright Edafe, ne ya yi wannan kira yayin da yake kira ga yan Najeriya da su dauki binciken arzikin da ba a gamsu da su ba a matsayin matakin kare al’umma daga barazanar garkuwa da mutane, kashe-kashe don kudin asiri, da zamba.

Yan sanda za su fara binciken tushen arzikin mutane
Yan Sanda Za Su Fara Kama Duk Wanda Ba a San Tushen Arzikinsa Ba Hoto: @Brightgoldenboy
Asali: Twitter

A wata wallafa da ya yi a shafinsa na X (wanda aka fi sani da Twitter a baya) a ranar Lahadi, 3 ga watan Disamba, kakakin yan sandan ya koka kan yawan sace-sacen mutane, kashe-kashe don kudin jini da damfarar intanet.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Edafe ya rubuta:

"Abun bakin ciki ne matuka cewa mutane na ganin ba daidai ba ne a yi tambaya game da dukiyar da ake zargi na mutanen da ba za su iya yin bayani mai gamsarwa kan hanyar samun kudin shigarsu ba. Alhalin muna da shari'ar kashe-kashe don kudin jini, Satar mutane, har ma da damfara ta intanet. Mun fada ma jami'anmu da su yi abun da ya dace sannan kada a dauke shi a matsayin haryar tatsar kudi."

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Ana jimamin kashe bayin Allah a wurin Maulidi, wani abu ya fashe a jihar APC

Rubutun nasa ya sa mutane tofa albarkacin bakunansu a soshiyal midiya.

An kama wasu kan kisan dan'uwansu

A wani labarin kuma, Legit Hausa ta rahoto a baya cewa yan sanda sun kama wasu maza biyu kan zargin rufe dan uwansu mai shekaru 35, Mohammed Sani tare da horar da shi da yunwa har lahira kan zarginsa da ake yi da maita a jihar Nasarawa.

Mukaddashin kwamishinan yan sandan jihar, Shettima Muhammad, wanda ya bayyana hakan ya ce an rufe Sani a dakinsa inda aka yi masa horo da yunwa har lahira bayan an dare hannaye da kafafunsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel