Biloniya Abdulsamad Rabiu Ya Ki Karban Babban Mukami a Gwamnatin Tinubu

Biloniya Abdulsamad Rabiu Ya Ki Karban Babban Mukami a Gwamnatin Tinubu

  • Shugaban rukunin kamfanonin BUA ya ki karban tayin shiga kwamitin kudi na Tinubu
  • Attajirin dan kasuwar ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da kamfaninsa ya saki a ranar Juma'a
  • Kamfanin ya yi ikirarin cewa ba a tuntubi Rabiu ba kafin a kasa sunansa a cikin jerin yan kwamitin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Shugaban rukunin kamfanonin BUA, Abdulsamad Rabiu, ya zabi kin amsa tayin shiga kwamitin kudi da jam'iyyar APC ta kafa.

A cikin wata sanarwa da kamfaninsa ya saki a ranar Juma'a, 1 ga watan Disamba, 2023, Mista Rabiu ya nuna sha'awarsa na son ci gaba da nisantan lamuran siyasa.

Abdul Samad ya ki shiga kwamitin kudi na Tinubu
Biloniya Abdulsamad Rabiu Ya Ki Karban Babban Mukami a Gwamnatin Tinubu Hoto: BUA Group, StateHouse
Asali: Twitter

Duk da kasancewarsa na kusa da Shugaban kasa Bola Tinubu, ya yanke shawarar kin amincewa da tayin kasancewa a kwamitin kudin mai mutum 34, wanda aka kafa a ranar Alhamis da ta hada da sauran yan kasuwa da fitattun yan jam’iyyar.

Kara karanta wannan

Gwamnan Bauchi Bala Mohammed ya yi ganawar sirri da Wike kan zaben 2027, rahoto

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An sanya sunan Rabiu ba tare da an tuntube shi ba

Kamar yadsa rukunin kamfanin BUA ya sanar a X (wanda aka fi sani da Twitter a baya), jam'iyyar mai mulki ta sanya sunan Mista Rabiu a jerin ba tare da ta tuntube shi ba.

Sanarwar ta kuma ambaci cewa Rabiu ya jajirce wajen bunkasa tattalin arziki ta kamfanin BUA da kuma bayar da gudunmawa ga ayyukan jin kai ta ASR Africa.

Wani bangare na jawabin na cewa:

Dangane da wannan, muna sanar da mawallafan, abokan aikinmu, masu ruwa da tsaki, da sauran jama'a cewa Mista Rabiu ya yanke shawarar kin amincewa da nadin/mukamin.

An yanke wannan shawarar ne bisa la'akari da cewa tun a baya ba a tuntube shi ba dangane da shigar da sunansa cikin jerin da kuma rashin lokaci saboda jadawali da yake bukata.

Kara karanta wannan

Kakakin Majalisar Wakilai ya karanto sunayen sabbin shugabannin kwamitoci 27 da mataimaka

Sauran yan kwamiti

Kamar yadda jerin sunayen da APC ta saki a ranar Juma'a ya nuna, An saka sunan Rabiu ne tare da sauran masu ruwa da tsaki.

Kamar yadda aka bayyana a cikin jerin, Uguru Ofoke ne zai jagoranci kwamitin kudin, yayin da Bashir Gumel zai kasance sakatare.

Manyan mutanen sun hada da shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio; shugaban majalisar wakilai, Abbas Tajudeen; Ministan Kudi kuma Ministan Tattalin Arziki, Wale Edun; da shahararren dan kasuwar mai A.A. Rano.

Bugu da kari, yan kasuwa irin su Mohammed Indimi, Kunle Soname, da Tein Jack Rich duk mambobi ne a kwamitin.

BUA zai bude sabon kamfanin siminti

A wani labarin, Legit Hausa ta kawo a baya cewa daya daga cikin manyan masu sarrafa siminti a Nigeria, kamfanin BUA, mallakin Abdul Samad Rabiu, ya bayyana shirin da yake yi na bude sabon kamfanin sarrafa siminti a jihar Sokoto a watan Janairu, 2023.

Rabiu, shugaban rukunin kamfanonin BUA, ya bayyana hakan a wata ziyara da ya kai wa gwamnan jihar Sokoto Ahmad Aliyu a ranar Laraba, Legit ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng