Gobara Ta Tashi a Gidan Talabijin Na NTA, Bayanai Sun Fito

Gobara Ta Tashi a Gidan Talabijin Na NTA, Bayanai Sun Fito

  • An samu tashin gobara a tashar gidan talabijin na ƙasa (NTA) da ke Sokoto a ranar Lahadi, 3 ga watan Disamban 2023
  • NTA a cikin wata sanarwa da ta fitar ta tabbatar da tashin gobarar inda ta ce ta shafe fiye da tsawon sa'o'i uku kafin a shawo kanta
  • A cikin sanarwar an yi nuni da cewa gobarar ba ta yi wata ɓarna ba sosai a tashar inda ma'aikata da jami'an hukumar kashe gobara suka yi nasarar kashe ta

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Sokoto - Gobara ta tashi a wani sashe na ofishin gidan talabijin na Najeriya (NTA) a Sokoto.

An dai bayyana cewa gobarar ta lalata wasu sassa na ginin tashar gidan talabijin ɗin na NTA.

Kara karanta wannan

Tinubu ya siya hannun jarin Atiku na $100m a kamfanin Intels? Fadar shugaban kasa ta yi magana

Gobara ta tashi a tashar NTA Sokoto
Gobara ta tashi a tashar talabijin ta NTA a Sokoto (Hoton ba na inda lamarin ya auku ba ne) Hoto: @dailytrust
Asali: Twitter

NTA a cikin wata sanarwa da ta fitar ta shafinta na X a ranar Lahadi, 3 ga watan Disamba ta tabbatar da tashin gobarar wacce ta ɗauki tsawon sa'o'i kafin a kashe ta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

"Ƙoƙarin ma'aikata da jami'an hukumar kashe gobara ya sanya an kashe gobarar da ta ƙona wasu sassan ginin tashar NTA Sokoto."
"Gobarar wacce ta ɗauki fiye da sa'o'i uku an samu shawo kanta, sannan ba ta shafin situdiyo, kayan aiki da sauran sassa masu muhimmanci ba."
"Binciken farko da injiniyoyi suka gudanar ya nuna cewa mai yiwuwa gobarar ta tashi ne sakamakon wutar lantarki."
"An kuma ceto motar kayan sauti, kayan aiki da kayan ofis daga gobarar."

Gobara ta tashi a sakatariyar gwamnatin tarayya

An samu tashin gobara a sakatariyar gwamnatin tarayya da ke babban birnin tarayya Abuja inda ta shafi wasu ofisoshi.

Kara karanta wannan

Gobara ta tashi a sakatariyar gwamnatin tarayya, bayanai sun fito

Daga cikin ofisoshin da gobarar ta shafa har da na mai ba shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu shawara kan muradun cigaba mai ɗorewa (SDG).

Gobara Ta Kone Shaguna da Masallaci

A wani labarin kuma, kun ji cewa shaguna da kayayyaki masu daraja da kudinsu ya kai miliyoyi sun lalace a Bakin Kasuwa da ke karamar hukumar Hadejia ta jihar Jigawa.

Gobarar ta wacce ta tashi a ranar Juma'a ta ƙone shaguna uku da wani sashe na masallacin da ke unguwar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel