Manyan Labarai A Yau
Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar yin galaba kan 'yan ta'adda a jihohin Ƙaduna da Borno. Sojojin sun yi nasarar ceto mutanen da aka sace.
Jami'an hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) sun kai samame a kasuwar 'yan canji da ke Abuja. Sun cafke wasu 'yan kasuwa.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya dawo gida Najeriya daga ziyarar da ya kai kasashen waje. Shugaban kasan ya dawo ne bayan ya kwashe makonni a can.
Kakakin majalisar dokokin jihar Edo, Blessing Agbebaku, ya nemi yafiya kan rigimar da ta barke a majalisar biyo bayan dakatar da wasu mambobi uku da ya yi.
Shugaban kamfanin hada-hadar kirifto na Binance, Richard Teng, ya yi zargin cewa wasu mutane sun bukaci jami'an kamfanin su ba da cin hanci a Najeriya.
Babban bankin Najeriya (CBN) ya dakatar da karbar la'adar ajiya da bankuna ke yi a hannun abokan huldarsu. Bankin na CBN ya bayyana hakan ne a wata sanarwa.
Gwamnatin tarayya ta hannun karamin ministan lafiya da walwalar jama'a ta musanta rade-radin cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ba shi da lafiya.
Fadar shugaban kasa ta bayyana cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zai dawo gida Najeriya a ranar Laraba, 8 ga watan Mayu bayan ya kwashe kwanaki a waje.
Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu, ya yi rashin dan uwansa wanda ya riga mu gidan gaskiya. Shugaba Bola Tinubu ya yi ta'aziyya.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari