'Yan Sanda Sun Cafke Malamin Addinin da Ya Bankawa Gidan Matarsa Wuta

'Yan Sanda Sun Cafke Malamin Addinin da Ya Bankawa Gidan Matarsa Wuta

  • Rundunar ƴan sandan jihar Ekiti ta cafke wani malamin addinin musulunci, Ahmed Ojo, bisa zarginsa da bankawa gidan matarsa wuta
  • Rahotanni sun bayyana cewa Ahmed Ojo ya ƙona gidan ne bayan da matarsa ​​ta ƙi yarda da buƙatar da ya zo da ita su gudanar da Sallar dare
  • Matar ta ce ta lura malamin ya yi mankas ne lokacin da ya dawo gida sannan ya fara neman ta tashi su gudanar da Sallar dare

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Isua Ijesa, jihar Ekiti - Jami’an rundunar ƴan sandan jihar Ekiti sun cafke wani malamin addinin musulunci, Ahmed Ojo bisa zargin ƙona gidan matarsa ​​a unguwar Egbe Odo da ke Isua Ijesa.

Kara karanta wannan

An ƙara yi wa dakarun sojoji sama da 20 kisan gilla a Najeriya? Gaskiya ta bayyana

Matar mai suna Bosede Afolabi, ta bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar 27 ga watan Afrilu bayan da ta ƙi yarda su yi Sallar dare.

Malamin addinin musulunci ya kona gidan matarsa
'Yan sanda sun cafke Ahmed Ojo bayan ya kona gidan matarsa a Ekiti Hoto: @PoliceNG
Asali: Facebook

Meyasa malamin ya ƙona gidan matarsa?

A yayin wata hira da jaridar The Punch, Bosede ta ce mijin nata ya buƙaci su yi sallar dare a wajen ƙarfe 11:00 na dare amma ta ƙi yarda saboda ta gaji.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bosede ta ce ƙin amincewar da ta yi ya sa mijin nata ya fusata, wanda hakan ya sanya ya fara tayar da rigima.

Ta ce ta lura ya yi mankas ne wanda hakan ya sa ta gayyaci makwabta domin su ba shi haƙuri amma hakan bai samu ba.

Bosede ta bayyana cewa daga baya ta bar gidan inda ta kwanta a gidan makwabta.

An bankawa gida wuta cikin dare

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya ta yi martani kan zargin neman cin hancin $150m a hannun Binance

"Da tsakar dare wata yarinya daga unguwarmu ta zo ta ƙwanƙwasa gidan domin ta sanar da mu cewa gidana na ci da wuta kuma ga dukkan alamu mijina ne ya bankawa gidan wuta."
"Ni da wasu makwabta muka garzaya zuwa gidan, sai muka ga cewa duk ginin ya ƙone ƙurmus. Kafin mu samu taimako wajen kashe wutar, komai ya ƙone."

- Bosede Afolabi

Matar malamin ke ba shi matsuguni

Bosede ta bayyana cewa ita ta ke ba malamin addinin matsugunni tun da suka yi aure bayan mijinta na farko ya rasu.

A kalamanta:

"Abin da na lura da shi a wannan daren shi ne ya sha ne ya yi mankas, wanda hakan a sanya na yi ƙoƙarin ka da saɓanin mu ya yi ƙamari."
"Wasu lokutan a buge yake dawowa gida amma ba mu taɓa samun wani rashin fahimta mai girma ba a baya."

Me ƴan sanda suka ce kan lamarin?

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da wani matashi, Abdullahi ya kashe matarsa kan ƙaramin abu

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar, Sunday Abutu, ya tabbatar da cewa wanda ake zargin yana hannun ƴan sanda kuma ana gudanar da bincike kan lamarin.

Shi dai wannan magidanci yana auren je-ka-da-kwarinka ne, matarsa ke da wurin zaman.

Miji ya yi yunƙurin hallaka matarsa

A wani labarin kuma, kun ji cewa wani magidanci ya shiga hannun jami'an tsaro biyo bayan mummunan yunƙurin da ya yi na hallaka matarsa a jihar Bauchi.

Magidancin wanda ɗan kasuwa ne dai ya yi yunƙurin halaka matar tasa ne domin ya sayar da talabijin ɗinsu ya ƙara jari a shagonsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel