Daga Karshe an Bayyana Lokacin Dawowar Tinubu Gida Najeriya

Daga Karshe an Bayyana Lokacin Dawowar Tinubu Gida Najeriya

  • Fadar shugaban ƙasa ta sanar da cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai dawo gida Najeriya a ranar Laraba, 8 ga watan Mayun 2024
  • Shugaban ƙasan dai ya kwashe kwanaki ba shi a cikin ƙasar nan bayan ya halarci wani taro a birnin Riyadh na ƙasar Saudiyya
  • Hakan ya jawo cece-kuce inda wasu ke tunanin cewa ko ya wuce birnin Paris ne domin a duba lafiyarsa a can

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Fadar shugaban ƙasa a ranar Talata, 7 ga watan Mayu, ta bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu zai dawo Najeriya ranar Laraba, 8 ga watan Mayu daga nahiyar Turai.

A cewar Bayo Onanuga, mai ba shugaban ƙasa shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, Shugaba Tinubu zai dawo Najeriya tare da hadimansa.

Kara karanta wannan

Tinubu yana kasar waje saboda rashin lafiya? Minista ya fadi gaskiya

Bola Tinubu zai dawo Najeriya
Shugaba Bola Tinubu zai dawo Najeriya daga nahiyar Turai Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

Bayo Onanuga ya bayyana hakan ne a wani rubutu da ya yi a shafinsa na manhajar X (wanda a baya aka fi sani da Twitter).

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu tare da hadimansa za su dawo Najeriya gobe daga nahiyar Turai."

- Bayo Onanuga

Kwanaki nawa Tinubu ya yi a waje?

Ranar Talata, 7 ga watan Mayu, ta yi daidai da cikar kwanaki takwas bayan Tinubu ya halarci taron tattalin arziƙi na duniya a birnin Riyadh na ƙasar Saudiyya.

Sai dai, har yanzu shugaban ƙasan bai dawo Najeriya ba tun bayan kammala taron.

Taron na kwanaki biyu, an buɗe shi ne a ranar Lahadi, 28 ga watan Afrilu, kuma ya kare a ranar Litinin, 29 ga watan Afrilu, 2024.

Ba a ji ɗuriyar shugaba Tinubu ba

Fadar shugaban ƙasar dai ba ta fitar da wata sanarwa kan abin da ya hana shugaban ƙasan dawowa gida Najeriya ba.

Kara karanta wannan

An shiga jimami bayan Nuhu Ribadu ya yi babban rashi a rayuwarsa

Hakan ya haifar da cece-ku-ce a wasu ɓangarori inda har wasu ke cewa mai yiwuwa Shugaba Tinubu ya zarce zuwa birnin Faris na ƙasar Faransa, inda a baya ya je aka duba lafiyarsa.

Mataimakin Tinubu, Kashim Shettima, ya shirya zuwa Amurka domin wakiltar shugaban ƙasan a wajen wani taro.

Idan za a tuna, amma ba zato ba tsammani ya soke tafiyar, inda ya dora alhakin hakan kan matsalar da jirgin saman ya samu.

SERAP tana shirin kai Tinubu kotu

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙungiyar SERAP ta buƙaci shugaban ƙasa Bola Tinubu ya janye maganar saka harajin 0.5% ga abokan hulɗar bankuna.

Ƙungiyar SERAP ta bayyana cewa lauyanta, Ebun-Olu Adegboruwa a shirye yake tsaf domin shigar da larar gwamnatin idan ta ƙi janye dokar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel