Manyan Labarai A Yau
Hamshakin attajiri kuma dan kasuwa, Prince Arthur Eze, ya bukaci 'yan Najeriya da su marawa gwamnatin shugaban kasa Bola Tinubu baya domin ta yi nasara.
Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) reshen jihar Zamfara ta caccaki masu ganin hukumar yaki da cin hanci ta binciki karamin ministan tsaro, Bello Matawalle.
Jigo a jam'iyyar All Progressives Congress (APC) Alhaji Musa Iliyasu Kwankwaso, ya bukaci manyan masu ruwa da tsaki na Arewacin Najeriya su marawa Tinubu baya.
Wata gobara ta tashi a gidan tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau a cikin daren ranar Lahadi. Gobarar ta lalata wani daki a cikin gidan.
Wani tsagin jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) ya shigar da kara a gaban hukumar EFCC kan Rabiu Musa Kwankwaso da wasu mutum 13 kan zargin N2.5bn
Wani jigo a babbar jam'iyyar adawa ta Peoples Democratuc Party (PDP) ya fadi dalilin da ya sanya jam'iyyar ba ta hukunta tsohon gwamnan Rivers Nyesom Wike ba.
Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya bukaci 'yan Najeriya da su kara hakuri da halin da tattalin arzikin kasar nan yake ciki a yanzu.
Hizbullah ta harba rokoki ga Isra'ila bayan wani hari da Isra'ila ta kai a wani kauye da ke kudancin Lebanon a ranar Lahadi wanda ya yi silar mutuwar mutane da dama.
Gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara, ya bayyana cewa rikicin siyasar da ya dabaibaye jihar ya zo karshe. Gwamnan ya ce yanzu lokacin gudanar da mulki ne.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari