EFCC Ta Cafke Wasu 'Yan Canji Yayin da Darajar Naira Ta Yi Raga Raga a Kasuwa

EFCC Ta Cafke Wasu 'Yan Canji Yayin da Darajar Naira Ta Yi Raga Raga a Kasuwa

  • Jami'an hukumar hana yaƙi da yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa (EFCC) sun kai samame a kasuwar ƴan canji da ke birnin tarayya Abuja
  • Jami'an na EFCC waɗanda suka fuskanci turjiya daga wajen ƴan kasuwar sun cafke wasu daga cikin ƴan canjin bayan an yi gumurzu
  • Hakan na zuwa ne yayin da darajar Naira ta ci gaba da faɗuwa ƙasa raga-raga a kasuwar canji inda ta koma N1,416/$

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Jami'an hukumar EFCC sun cafke wasu ƴan canjin kuɗi a kasuwar Wuse Zone 4 da ke birnin tarayya Abuja, ranar Talata.

Hakan na zuwa ne yayin da darajar Naira ta ci gaba da faɗuwa raga-raga a kasuwar canji.

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya ta yi martani kan zargin neman cin hancin $150m a hannun Binance

EFCC ta dira kan 'yan canji
Jami'an EFCC sun cafke wasu 'yan canji a Abuja Hoto: EFCC
Asali: Twitter

Ya aka ƙare tsakanin ƴan canji da EFCC?

Jaridar The Punch ta ce wasu ƴan kasuwar sun bayyana cewa wasu daga cikin ƴan canjin sun yi fito na fito da jami'an EFCC a lokacin samamen.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jami'an na EFCC na yawan kai samame a kasuwar domin tsarkake ta daga waɗanda ake zargin suna yin gurɓataccen kasuwanci, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

Sai dai, jami'an sun fuskanci turjiya daga wajen ƴan kasuwar wanda hakan ya sanya aka yi harbe-harbe tare da lalata motar jami'an na EFCC.

Wani ganau ba jiyau ba ya bayyana cewa:

"Jami'an EFCC sun kawo samame domin cafke mutane a ranar Litinin, kuma sun zo a ranar Talala, amma samamen da suka kawo na ranar Talata ya fi zafi."
"Wannan shi ne abin da muke fuskanta. A ranar Litinin sun kama ƴan kasuwa amma a ranar Talata mutane sun kai musu farmaki sannan an yi harbin bindiga saboda mutanen mu sun yi turjiya."

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: An kama 'yan canji 17 a kasuwar musayar kuɗi a jihar Kano

"Mutane sun harzuƙa tare da fusata. Har fasa gilasan motocin jami'an EFCC suka yi wanda hakan ke nuna cewa an ƙure haƙurinsu."

Darajar Naira ta ci gaba da faɗuwa

Sai dai, duk da cafke mutanen da EFCC ke yi domin darajar Naira ta farfaɗo, saɓanin hakan ake ta samu inda Naira ta ci gaba da faɗuwa ƙasa raga-raga.

A kasuwar canjin Naira ta koma N1,416 kan Dala ɗaya daga N1,354 kan Dala ɗaya da aka siyar da ita a ranar Litinin.

Sabon farashin ya nuna cewa darajar Naira ta faɗi da kaso 4.4% ko N62 wanda hakan ya sanya damuwa kan rashin tabbas ɗin darajarta.

Naira ta farfaɗo a kasuwannin canji

A baya labari ya zo cewa Naira ta samu daraja sosai a kasuwar canji ta gwamnati da ta bayan fage biyo bayan faɗuwar darajar Dalar Amurka.

Wannan na zuwa ne bayan da babban bankin Najeriya (CBN) ya sanar da kammala biyan duk wani bashi na kuɗin waje da ake binsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel