'Yan Bindiga Sun Hallaka Kwamandan Rundunar NSCDC Yayin Fafatawa a Benue

'Yan Bindiga Sun Hallaka Kwamandan Rundunar NSCDC Yayin Fafatawa a Benue

  • An gwabza faɗa tsakanin jami'an tsaro da miyagun ƴan bindiga ɗauke da makamai a ƙauyen Shaapera da ke ƙaramar hukumar Gwer ta Yamma a jihar Benue
  • Ƙazamin artabun da aka yi ya jawo ƴan bindiga sun hallaka wani kwamandan rundunar NSCDC mai suna Mike Ode
  • Sai dai, jami'an tsaron sun yi nasarar hallaka ƴan bindiga sama da 10 a ƙazamin faɗan da aka yi da masu tada ƙayar bayan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Benue - Ƴan bindiga ɗauke da makamai sun kashe wani kwamandan na rundunar NSCDC a jihar Benue.

Kwamandan da ƴan bindigan suka hallaka an bayyana sunansa a matsayin Mike Ode.

'Yan bindiga sun hallaka kwamandan NSCDC
'Yan bindiga sun kashe kwamandan NSCDC a Benue Hoto: @OfficialNSCDC
Asali: Twitter

Jaridar The Punch ta ce lamarin ya faru ne a ƙauyen Shaapera da ke ƙaramar hukumar Gwer ta Yamma a jihar.

Kara karanta wannan

An ƙara yi wa dakarun sojoji sama da 20 kisan gilla a Najeriya? Gaskiya ta bayyana

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda ƴan bindiga suka kashe jami'in NSCDC

Kawun marigayin, Nicholas Ode, ya bayyana cewa an kashe ɗan uwansa ne a ƙauyen Shaapera da ke ƙaramar hukumar Gwer ta Yamma a ranar Litinin.

Ya ƙara da cewa an ajiye gawarsa a ɗakin ajiye gawa na asibitin koyarwa na jami’ar jihar Benue da ke Makurdi, cewar rahoton Ripples Nigeria.

"An gaya mana cewa ya je aiki na musamman a ƙauyen Shaapera. A can ne suka yi arangama da ƴan bindiga kuma a yayin da ake artabun, jami’an NSCDC sun samu nasarar kashe ƴan bindiga har 10."
"Abin takaici, an gaya mana cewa an kashe ɗaya daga cikin jami’an NSCDC guda huɗu, wanda ɗan uwana ne, yayin da sauran suka tsira."

- Nicholas Ode

Me NSCDC ta ce kan lamarin?

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar NSCDC, Mike Ejelikwu, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce mutuwar jami’an ba za ta hana rundunar gudanar da aikinta na samar da tsaro ga duk wani ɗan kasa mai bin doka da oda a jihar ba.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun samu galaba kan 'yan ta'adda yayin wani artabu

Ya ƙara da cewa marigayin ya rasu yayin artabu da ƴan bindiha sannan ya tabbatar da cewa an yi wa ƴan bindigan illa sosai.

Ƴan bindiga sun farmaki makaranta

A wani labarin kuma, kun ji cewa miyagun ƴan bindiga sun kai hari makarantar sakandiren Father Angus Frazer Memorial High School da ke ƙauyen Adeke a jihar Benue.

Maharan waɗanda ba a san ko su waye ba sun yi wa mai gadin da ke bakin aiki mummunan rauni a harin da suka kai cikin dare.

Asali: Legit.ng

Online view pixel