Labarin Sojojin Najeriya
Rundunar sojin Najeriya ta kwato makamai a hannun yan ta'adda a jihohin Imo da Kwara. Rundunar ta yi nasarar cafke wasu manyan yan bindiga a jihohin yayin farmakin.
Hedikwatar tsaro ta Najeriya ta bayyana cewa an samu karuwar wadanda suka rasu a harin da 'yan ta'adda su ka kai Gwoza, yayin da wasu mutane 20 su ka rasu.
Dakarun hadin gwiwa na kasashe masu yaki da Boko Haram (MNJTF) sun fatattaki maboyar miyagu a iyakokin kasar nan da Kamaru da tafkin Chadi, kuma sun yi nasara.
Rundunar sojin saman Najeriya tace babu jirginta mai saukar ungulu da yayi haɗari. Tace jirgin aiki ne mara matuƙi ya rikito a ƙauyen Rumji dake kusa da sansaninta.
Jirgin dakarun sojin saman Najeriya ya tafka hatsari a ƙauyen Tani dake ƙaramar hukumar Igabi ta jihar Kaduna. Matuƙin jirgin cikin gwanancewa ya tsira da ransa.
Dakarun rundunar sojojin saman Najeriya sun samu nasarar tarwatsa barayin man fetur a jihar Rivers. Sojojin sun kuma hallaka 'yan ta'adda a jihar Neja.
Rahotannin da muke samu a safiyar yau Lahadi na nuni da cewa Allah ya yiwa tsohon babban hafsan tsaron Najeriya, Ibrahim Ogohi rasuwa yana da shekara 76 a duniya.
Rundunar sojin Najeriya ta fafata da yan bindiga a jihar sokoto inda ta kashe guda biyar tare da kwato mutane biyu da suka yi garkuwa da su a karamar hukumar Gudu.
Hedkwatar tsara ta kasa (DHQ) ta bayyana nasarar da dakarun sojojin Najeriya suka samu kan 'yan ta'adda daga watan Afirilu zuwa watan Yunin shekarar 2024.
Labarin Sojojin Najeriya
Samu kari